Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Ya rushe Haikalinsa kamar bukka cikin gona, Ya mai da wurin yin ƙayyadaddun idodinsa kufai. Ubangiji ya sa ƙayyadadden idi da kiyaye Asabar Su ƙare a Sihiyona, Da zafin fushinsa kuma ya wofinta sarki da firist.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ya rushe haikalinsa kamar lambu; ya hallaka wurin yi masa sujada. Ubangiji ya sa Sihiyona ta manta da bukukkuwanta da kuma ranakunta na Asabbaci; a cikin zafin fushinsa ya watsar da sarki da firist.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:6
25 Iomraidhean Croise  

Sun sa wa Haikalinka wuta, Sun ƙazantar da wurin da akan yi maka sujada, Sun farfashe shi duk.


Wurin zamansa yana Urushalima, A dutsen Sihiyona zatinsa yake.


Me ya sa ka rushe shingen da yake kewaye da ita? Ga shi yanzu, duk mai wucewa yana iya satar 'ya'yanta.


Ka rurrushe garun birninsa, Ka mai da sansaninsa mai kagara kufai.


Ko kusa ba na bukatar hadayunku marasa amfani. Ina jin ƙyamar ƙanshin turaren da kuke miƙawa. Ba zan jure da bukukuwanku na amaryar wata, da na ranakun Asabar, da taronku na addini ba, duka sun ɓaci saboda zunubanku.


Urushalima kaɗai ta ragu, birnin da aka kewaye da yaƙi, ba wata kariya kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi, ko ta mai ƙumu a gonar kankana.


Zan musunci masu mulkin tsattsarkan masujadai, Saboda haka zan jawo wa Isra'ila hallaka, Zan bari a la'anta mutanena su sha zagi!”


“Ga abin da zan yi wa gonar inabina. Zan cire shingen da yake kewaye da ita, in rushe bangon da ya kāre ta, in bar namomin jeji su cinye ta, su tattake ta.


Zan bar ciyayi su rufe ta. Ba zan yi wa kurangar inabin aski ba, ko in yi mata noma, amma zan bar sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa su rufe ta. Har ma zan sa gizagizai su hana ta ruwan sama.”


Abokan gabanmu sun kusa su kori mutanenka gaba ɗaya sun kuma tattake Haikalinka.


Haikalinmu, kyakkyawan keɓaɓɓen wuri inda kakanninmu suka yi yabonka, aka lalatar da shi da wuta, dukan wuraren da muka ƙauna aka lalatar da su.


Amma idan ba ku kasa kunne gare ni ba, ba ku kuwa kiyaye ranar Asabar da tsarki ba, kun kuma ɗauki kaya kun shiga ta ƙofofin Urushalima a ranar Asabar, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wuta. Za ta kuwa cinye fādodin Urushalima, ba kuwa za ta kasu ba.’ ”


“Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa'ad da kuka tafi Masar. Za ku zama najasa, da abin ƙyama, da la'ana, da abin ba'a. Wannan wuri kuwa ba za ku ƙara ganinsa ba.’


“Sai ka faɗa wa Baruk cewa, ‘Ni Ubangiji na ce, ga shi, abin da na gina zan rushe shi, abin da kuma na dasa zan tumɓuke shi, wato ƙasar ɗungum.


Ku ji, sun gudu sun tsere daga ƙasar Babila, Don su faɗa cikin Sihiyona, Sakayyar Ubangiji Allahnmu domin Haikalinsa.


Hanyoyin Sihiyona suna baƙin ciki Domin ba mai halartar ƙayyadaddun idodi. Dukan ƙofofinta sun zama kufai, Firistocinta suna nishi, Budurwanta kuma suna wahala, Ita kanta ma tana shan wuya ƙwarai.


Ubangiji kansa ya watsar da su, Ba zai ƙara kulawa da su ba. Ba su darajanta firistoci ba, Ba su kuma kula da dattawa ba.


Shi wanda muke dogara gare shi, Wato zaɓaɓɓe na Ubangiji, ya auka cikin raminsu, Shi wanda muka ce, “A ƙarƙashin inuwarsa ne za mu zauna a cikin sauran al'umma.”


An rataye shugabanni da hannuwansu, Ba a kuma girmama dattawa ba.


Bai kuwa cika rantsuwarsa da alkawarinsa ba. Ya ƙulla alkawari, amma ga shi, ya aikata dukan waɗannan abubuwa, ba zai kuɓuta ba.


Zan sa biranenku su zama kangwaye, in mai da wuraren yin sujada kufai, ba zan shaƙi ƙanshin turarenku ba.


Zan tara waɗanda suka yi makoki domin idi, Waɗanda suke tare da ke, Wato waɗanda nawayar zaman talala Ta zamar musu abin zargi.


Saboda haka, ni ma zan sa jama'ar Isra'ila su raina ku, su ƙasƙantar da ku a gaban dukan mutane, domin ba ku kiyaye umarnina ba, sa'ad da kuke koyar da nufina, kun yi tara.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan