Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Ubangiji ya zama kamar maƙiyi, ya hallaka Isra'ila. Ya hallaka fādodinta duka, Ya mai da kagaranta kango. Ya aukar wa Yahuza da makoki da baƙin ciki mai yawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Ubangiji kamar maƙiyi ne; ya hallaka Isra’ila. Ya hallaka wurarenta duka ya kuma hallaka kagaranta. Ya ƙara yawan makoki da baƙin ciki wa Diyar Yahuda.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:5
17 Iomraidhean Croise  

Ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gidajen urushalima. Ya ƙone kowane babban gida.


“Me ya sa kake guduna? Me ya sa ka maishe ni kamar maƙiyi?


Allah ya zaburo mini da fushi, Ya maishe ni kamar mafi mugunta daga cikin maƙiyansa.


Ka rurrushe garun birninsa, Ka mai da sansaninsa mai kagara kufai.


Dukan waɗanda suke wucewa za su sace masa kayansa, Maƙwabtansa duka suna yi masa ba'a.


sa'an nan Allah zai kawo wa birnin wanda ake ce da shi, “Bagaden Allah,” masifa. Za a yi kuka a yi kururuwa, birnin kansa za a maishe shi bagade inda za a ƙona hadayun ƙonawa!


amma suka i masa tayarwa, suka cika shi da ɓacin rai. Saboda haka Ubangiji ya yi gāba da su, ya kuwa yi yaƙi da su.


Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da a ce Musa da Sama'ila za su tsaya a gabana, duk da haka zuciyata ba za ta komo wurin mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana su yi tafiyarsu!


“Ku faɗa wa Zadakiya, Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ga shi, zan juyo kayan yaƙin da suke hannunka waɗanda kake yaƙi da su gāba da Sarkin Babila, da sojojinsa, waɗanda suka kewaye garun birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan.


Dukan masu ƙaunarku sun manta da ku, Ba su ƙara kulawa da ku, Domin na yi muku bugu irin na maƙiyi. Na yi muku horo irin na maƙiyi marar tausayi, Domin laifofinku masu girma ne, Domin zunubanku da yawa suke.


Sai ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan manyan gidajen da suke Urushalima.


Dukan wuraren zaman Yakubu, Ubangiji ya hallakar ba tausayi, Da fushinsa kuma ya rurrushe kagaran Sihiyona. Ya ƙasƙantar da mulki da masu mulkin.


Ya ja bakansa kamar abokan gāba, Ya kuma nuna ikonsa kamar maƙiyi. Ya hallaka dukan abin da yake da bansha'awa. A alfarwar Sihiyona, ya zubo da hasalarsa kamar wuta.


Ya buɗe littafin a gabana, akwai rubutu ciki da baya. Ba abin da aka rubuta sai maganganun baƙin ciki, da makoki, da kaito.


Sai Sama'ila ya ce masa, “Don me za ka tambaye ni, tun da yake Ubangiji ya rabu da kai, ya zama magabcinka?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan