Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Ya ja bakansa kamar abokan gāba, Ya kuma nuna ikonsa kamar maƙiyi. Ya hallaka dukan abin da yake da bansha'awa. A alfarwar Sihiyona, ya zubo da hasalarsa kamar wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Kamar abokin gāba, ya ɗana bakansa; hannun damansa na shirye. Kamar maƙiyi, ya kashe duk wanda idonsa ya ji daɗin gani; ya zuba fushinsa kamar wuta a kan tenti na Diyar Sihiyona.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:4
38 Iomraidhean Croise  

“Ku tafi ku yi tambaya a wurin Ubangiji domina, da kuma domin sauran waɗanda suka ragu a Isra'ila da Yahuza, a kan abin da littafin da aka gāno ya faɗa, gama Ubangiji ya yi fushi da mu da hasala mai tsanani saboda kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji, su aikata bisa ga dukan abin da aka faɗa a wannan littafi ba.”


Da yake sun bar bina suka ƙona turare ga gumaka domin su sa ni in yi fushi da dukan ayyukan hannuwansu, saboda haka zan yi fushi da wannan wuri, ba kuwa zan huce ba.’


Allah ya zaburo mini da fushi, Ya maishe ni kamar mafi mugunta daga cikin maƙiyansa.


Allah Maɗaukaki ya harbe ni da kibau, Dafinsu kuwa ya ratsa jikina. Allah ya jera mini abubuwa masu banrazana.


Mugaye sun zare takuba, Sun tanƙware bakkunansu Don su kashe matalauta da masu bukata, Su karkashe mutanen kirki.


Zai ɗana bakansa ya shirya shi, Zai ɗauki makamansa masu dafi, Ya kuma auna kibansa masu wuta.


Domin haka ya sa mu ji zafin fushinsa, Mu kuma sha wahalar da yaƙi ya kawo. Fushinsa ya yi ƙuna cikin dukan Isra'ila kamar wuta, Amma ba mu taɓa sanin abin da yake faruwa ba, Ba mu koyi kome daga wannan ba ko kaɗan.


amma suka i masa tayarwa, suka cika shi da ɓacin rai. Saboda haka Ubangiji ya yi gāba da su, ya kuwa yi yaƙi da su.


Da fushina na tattake dukan sauran al'umma, na farfashe su. Na kwararar da jinin ransu a ƙasa.”


An lalatar da alfarwata, Dukan igiyoyi sun tsintsinke, 'Ya'yana maza sun bar ni, ba su nan. Ba wanda zai kafa mini alfarwata Ya kuma rataya labulena.


“ ‘Ya gidan Dawuda, ni Ubangiji na ce, Ku aikata adalci kowace safiya. Ku ceci wanda aka yi masa ƙwace daga hannun mai matsa masa, Don kada hasalata ta tashi kamar wuta, Ta yi ƙuna, har ba mai iya kashe ta, Saboda mugayen ayyukanku.


Ni kaina zan yi yaƙi da kai da dukan ƙarfina, da hasalata, da dukan zafin fushina.


Dukan masu ƙaunarku sun manta da ku, Ba su ƙara kulawa da ku, Domin na yi muku bugu irin na maƙiyi. Na yi muku horo irin na maƙiyi marar tausayi, Domin laifofinku masu girma ne, Domin zunubanku da yawa suke.


Mai yiwuwa ne za su roƙi Ubangiji, su tuba, su bar mugayen ayyukansu, gama Ubangiji yana fushi ƙwarai, Ubangiji ya hurta hasala a kan wannan jama'a.”


Ya ku mutanen Yahuza da na Urushalima, Ku yi wa kanku kaciya domin Ubangiji, Ku kawar da loɓar zukatanku Don kada fushina ya fito kamar wuta, Ya cinye, ba mai iya kashewa, Saboda mugayen ayyukan da kuka aikata.”


“Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa'ad da kuka tafi Masar. Za ku zama najasa, da abin ƙyama, da la'ana, da abin ba'a. Wannan wuri kuwa ba za ku ƙara ganinsa ba.’


Saboda haka ga abin da Ubangiji Allah ya ce, “Duba, zan kwarara fushina da hasalata a kan wannan wuri, a kan mutum duk da dabba, da akan itatuwan saura da amfanin gona. Zai yi ta cin wuta, ba kuwa za a kashe ba.”


“Daga sama ya aukar da wuta a cikin ƙasusuwana. Ya kuma kafa wa ƙafafuna ashibta, Ya komar da ni baya, Ya bar ni a yashe, sumamme dukan yini.


Ubangiji ya zama kamar maƙiyi, ya hallaka Isra'ila. Ya hallaka fādodinta duka, Ya mai da kagaranta kango. Ya aukar wa Yahuza da makoki da baƙin ciki mai yawa.


Hakika ikonsa ya yi ta gāba da ni dukan yini.


Ƙaƙa zinariya ta zama duhu! Ƙaƙa zinariya tsantsa ta sāke! Tsarkakakkun duwatsu kuma suna zube A kowane magamin titi.


Ubangiji ya saki fushinsa, Ya zuba fushinsa mai zafi. Ya kunna wa Sihiyona wuta Wadda ta cinye harsashin gininta.


“Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce da hasalata zan sa babban hadiri mai iska, da rigyawa, da manyan ƙanƙara su hallaka shi.


da ƙarfi da yaji da fushi kuma, zan fito da ku daga cikin mutane, in tattaro ku daga sauran ƙasashe inda aka warwatsa ku.


Kamar yadda azurfa takan narke a cikin tanderu, haka kuma za ku narke, za ku sani ni, Ubangiji ne, na zubo muku da zafin fushina.”


“Kai ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu madogararsu, da murnarsu, da darajarsu, da abin da idanunsu suka ji daɗin gani, da abin da yake faranta zuciyarsu, da 'ya'yansu mata da maza,


Sai na husata da su saboda jinin da suka zuba a cikin ƙasar, da kuma yadda suka ƙazantar da ƙasar da gumakansu.


“‘Ta haka zan sa fushina ya huce, hasalata kuma a kansu ta lafa, ni kuma in wartsake. Sa'an nan za su sani ni Ubangiji na yi magana da zafin kishi sa'ad da na iyar da fushina a kansu.


Annoba za ta kashe wanda yake nesa, wanda yake kusa kuwa takobi zai kashe shi. Yunwa kuma za ta kashe wanda yaƙi ya kewaye shi. Ta haka zan aukar da fushina a kansu.


“Sun busa ƙaho, sun gama shiri duka, amma ba wanda ya tafi yaƙi, gama fushina yana kan dukan taron jama'a.


Zan yi gāba da ku in sa maƙiyanku su ɗibge ku, waɗanda suke ƙinku za su mallake ku. Za ku yi ta gudu ba mai korarku.


Ubangiji Allah mai kishi ne, mai sakayya, Ubangiji mai sakayya ne, mai hasala. Ubangiji yakan ɗauki fansa a kan maƙiyansa. Yana tanada wa maƙiyansa fushi.


Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa kuma zai iya daurewa da hasalarsa? Yana zuba hasalarsa mai kama da wuta, Duwatsu sukan farfasu a gabansa.


Gama fushina ya kama wuta, Tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za ta cinye duniya da dukan amfaninta, Za ta kama tussan duwatsu.


Sai Sama'ila ya ce masa, “Don me za ka tambaye ni, tun da yake Ubangiji ya rabu da kai, ya zama magabcinka?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan