Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Da zafin fushinsa, ya karya ƙarfin Isra'ila, Ya kuma bar yi musu taimako A lokacin da abokan gāba suka zo. Kamar harshen wuta, ya ƙone dukan abin da yake na Yakubu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 A cikin zafin fushi ya fasa kowane ƙaho na Isra’ila. Ya janye hannun damansa sa’ad da maƙiyi ya zo. Ya yi ƙuna a cikin Yaƙub kamar wuta mai ƙone duk abin da yake kusa da ita.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:3
25 Iomraidhean Croise  

Da yake sun bar bina suka ƙona turare ga gumaka domin su sa ni in yi fushi da dukan ayyukan hannuwansu, saboda haka zan yi fushi da wannan wuri, ba kuwa zan huce ba.’


“Ina makoki saye da tsummoki, Ina zaune cikin ƙura a kunyace.


A nan ne zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyar Dawuda Yake zama babban sarki, A nan ne kuma zan wanzar da Mulkin zaɓaɓɓen sarkina.


Me ya sa ka ƙi taimakonmu? Ka tasar musu ka hallaka su!


Shi zai karya ikon mugaye, Amma za a ƙara wa masu adalci ƙarfi.


Na dai faɗa musu su daina yanga, Su daina yin taƙama.”


Har yaushe za ka yi ta fushi da mu, ya Ubangiji? Har abada ne? Kullum ne fushinka zai yi ta ci kamar wuta?


Zan ƙaunace shi kullum, in amince da shi, Zan sa ya yi nasara kullayaumin.


Har yaushe za ka ɓoye kanka, ya Ubangiji? Har abada ne? Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta?


Daidai kamar yadda busasshen itacen da tartsatsin wuta ya fāɗa wa, haka mutane masu iko za su hallaka ta wurin mugayen ayyukansu, ba wanda zai iya hana a hallaka su.


Domin haka ya sa mu ji zafin fushinsa, Mu kuma sha wahalar da yaƙi ya kawo. Fushinsa ya yi ƙuna cikin dukan Isra'ila kamar wuta, Amma ba mu taɓa sanin abin da yake faruwa ba, Ba mu koyi kome daga wannan ba ko kaɗan.


Zan hukunta ku bisa ga ayyukanku,’ in ji Ubangiji, ‘Zan sa wa jejin ƙasar wuta. Za ta cinye duk abin da yake kewaye da ita.’ ”


Ya ku mutanen Yahuza da na Urushalima, Ku yi wa kanku kaciya domin Ubangiji, Ku kawar da loɓar zukatanku Don kada fushina ya fito kamar wuta, Ya cinye, ba mai iya kashewa, Saboda mugayen ayyukan da kuka aikata.”


An karye ikon Mowab da ƙarfinta, ni Ubangiji na faɗa.


Saboda haka ga abin da Ubangiji Allah ya ce, “Duba, zan kwarara fushina da hasalata a kan wannan wuri, a kan mutum duk da dabba, da akan itatuwan saura da amfanin gona. Zai yi ta cin wuta, ba kuwa za a kashe ba.”


“Daga sama ya aukar da wuta a cikin ƙasusuwana. Ya kuma kafa wa ƙafafuna ashibta, Ya komar da ni baya, Ya bar ni a yashe, sumamme dukan yini.


Ubangiji ya saki fushinsa, Ya zuba fushinsa mai zafi. Ya kunna wa Sihiyona wuta Wadda ta cinye harsashin gininta.


“Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce da hasalata zan sa babban hadiri mai iska, da rigyawa, da manyan ƙanƙara su hallaka shi.


“Sun busa ƙaho, sun gama shiri duka, amma ba wanda ya tafi yaƙi, gama fushina yana kan dukan taron jama'a.


Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa kuma zai iya daurewa da hasalarsa? Yana zuba hasalarsa mai kama da wuta, Duwatsu sukan farfasu a gabansa.


“Duba rana tana zuwa, sa'ad da dukan masu girmankai, da mugaye za su ƙone kamar tattaka, a ran nan za su ƙone ƙurmus ba abin da zai ragu, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Ya ta da Mai Ceto mai iko dominmu, Daga zuriyar baransa Dawuda.


Ƙwaryar shiƙarsa tana hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai sarai, ya taro alkama ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun sai ya ƙone shi a wuta marar mutuwa.”


Gama fushina ya kama wuta, Tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za ta cinye duniya da dukan amfaninta, Za ta kama tussan duwatsu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan