Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Ka gayyato mini tsoro Kamar yadda akan gayyato taro a ranar idi. A ranar fushin Ubangiji Ba wanda ya tsere, ko wanda ya tsira. 'Ya'yan da na yi renonsu, na goye su, Maƙiyina ya hallaka su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 “Kamar yadda kake yin gayyata a ranar biki, haka kake kawo mini tsoro a kowane gefe. A ranar fushin Ubangiji ba mai tserewa ba wanda zai tsira; maƙiyina ya kashe waɗanda na yi renonsu, na kuma lura da su.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:22
16 Iomraidhean Croise  

Don haka Ubangiji ya bashe su ga Sarkin Kaldiyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a Haikali, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka a hannunsa.


Na ji magabtana da yawa suna raɗa, Razana ta kewaye ni! Suna ƙulla maƙarƙashiya don su kashe ni.


Za ta yi ta auko muku a kai a kai kowace safiya. Tilas ku sha ta dare da rana. Kowane sabon jawabin da zai zo muku daga wurin Allah, zai kawo muku sabuwar razana!


Saboda haka ni Ubangiji na ce, ‘Ga shi, ina kawo musu masifa wadda ba za su iya tsere mata ba, ko da za su yi kuka gare ni ba zan ji su ba.


“Ka ƙi Yahuza ke nan ɗungum? Ranka kuma yana jin ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu, har da ba za mu iya warkewa ba? Mun zuba ido ga samun salama, amma ba wani abin alheri da ya zo. Mun kuma sa zuciya ga warkewa, amma sai ga razana.


Kashegari sa'ad da Fashur ya fitar da Irmiya daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “Ubangiji ba zai kira ka Fashur ba, amma ya ba ka suna Magormissabib, wato razana ta kowace fuska.


Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’


“Yanzu, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ina tambaya, me ya sa kuke jawo wa kanku wannan babbar masifa, kuna so ku hallakar da mata da maza, yara da jarirai daga cikin Yahuza, har a rasa wanda zai wanzu?


Ubangiji ya yi tambaya ya ce, “Me nake gani? Sun tsorata, suna ja da baya, An ci sojojinsu, suna gudu, Ba su waiwayen baya, akwai tsoro a kowane sashi.”


Kada ku fita zuwa gona, Kada kuma ku yi yawo a kan hanya, Gama abokin gāba yana da takobi, Razana a kowane sashi.”


“La'anannu ne 'ya'yanku, da amfanin gonakinku, da 'ya'yan shanunku, da 'ya'yan tumakinku da na awakinku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan