Makoki 2:21 - Littafi Mai Tsarki21 Yara da tsofaffi suna kwance cikin ƙurar tituna, An kashe 'ya'yana, 'yan mata da samari, da takobi. Ka kashe su a ranar fushinka, ba tausayi. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202021 “Matasa da tsofaffi duk suna kwanciya a cikin ƙurar tituna; an karkashe matasa da ’yan matana da takobi. Ka kashe su a ranar fushinka; ka kashe su ba tausayi. Faic an caibideil |
Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’
Don haka ina cike da fushin Ubangiji Na gaji da kannewa. Ubangiji ya ce, “Zan kwararo fushi kan yara da suke a titi. Da kuma kan tattaruwar samari. Za a ɗauke mata da miji duka biyu, Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufa tukub-tukub. Za a ba waɗansu gidajensu, da gonakinsu, da matansu, Gama zan nuna ikona in hukunta mazaunan ƙasar.