Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Ki tashi, ki ya ta kuka dukan dare, Ki bulbule abin da yake cikin zuciyarki Kamar ruwa gaban Ubangiji. Ki miƙa hannuwanki zuwa gare shi, Saboda rayukan 'ya'yanki, Waɗanda suke suma da yunwa A magamin kowane titi!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Ki tashi, ki yi kuka cikin dare, dare na yi sai ki fara kuka; kina buɗewa Ubangiji zuciyarki. Ki ɗaga hannuwanki gare shi domin rayukan ’ya’yanki, waɗanda suka suma don yunwa a kan kowane titi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:19
31 Iomraidhean Croise  

A maimakon cin abinci, sai baƙin ciki nake yi, Ba kuma zan daina yin nishi ba,


Da dare nakan tuna da kai, ya Ubangiji, Ina kuwa kiyaye dokarka.


Ku ɗaga hannuwanku sama, ku yi addu'a a Haikali, Ku yabi Ubangiji!


Ka karɓi addu'ata kamar turaren ƙonawa, Ka karɓi ɗaga hannuwa sama da na yi kamar hadayar maraice.


Na kawo masa dukan koke-kokena, Na faɗa masa dukan wahalaina.


Sa'ad da na yi niyyar fid da zuciya, Ya san abin da zan yi. A kan hanyar da zan bi Maƙiyana sun kafa mini tarko a ɓoye.


Ka ji ni lokacin da na yi kuka gare ka neman taimako, Ina ɗaga hannuwana wajen tsattsarkan Haikalinka.


Dare da rana ina kuka, Hawayena kaɗai su ne abincina, A kowane lokaci maƙiyana suna ta tambayata, “Ina Allahnka?”


Zuciyata takan ɓaci in na tuna da abin da ya wuce, Sa'ad da nakan tafi tare da taron jama'a zuwa Haikalin Allah, Ina bishe su a jere. Taron jama'a masu farin ciki, suna raira waƙa, Suna ta da murya, suna yabon Allah.


Ubangiji ya nuna madawwamiyar ƙaunarsa kowace rana! Ni ma in raira yabo gare shi kowane dare, In yi addu'a ga Allah, wanda ya ba ni rai.


Ya jama'ata, ku dogara ya Allah a kowane lokaci! Ku faɗa masa dukan wahalarku, Gama shi ne mafakarmu.


Muddin raina, zan yi maka godiya, Zan ta da hannuwana sama, in yi addu'a gare ka.


Da dare ina zuba ido gare ka da zuciya ɗaya. Sa'ad da kake yi wa duniya da jama'arta shari'a Dukansu za su san yadda adalci yake.


A kan kusurwar kowane titi Mutanenki sun rafke saboda rashin ƙarfi, Sun zama kamar barewa da tarkon maharbi ya kama. Suka ji ƙarfin fushin Allah.


Idan na tafi cikin saura, Sai in ga waɗanda aka kashe da takobi! Idan kuma na shiga birni, Sai in ga waɗanda suke ta fama da yunwa! Gama annabi da firist, sai harkarsu suke ta yi a ƙasar, Amma ba su san abin da suke yi ba.’ ”


Irmiya ya ce, “Ya ku mata, ku ji maganar Ubangiji, Ku kasa kunne ga maganar da ya faɗa, Ku koya wa 'ya'yanku mata kukan makoki, Kowacce ta koya wa maƙwabciyarta waƙar makoki,


Ubanni za su cinye 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su cinye ubanninsu. Zan hukunta ki, waɗanda kuma suka tsira zan watsar da su ko'ina.


Gama zan aiko miki da masifu na yunwa domin hallakarwa. Zan aiko miki da su don su hallaka ki. Zan kawo miki yunwa mai tsanani, in sa abincinki ya ƙare.


Ku aske kanku saboda ƙaunatattun 'ya'yanku. Ku yi wa kanku ƙwaƙwal kamar ungulu, Gama 'ya'yanku za su tafi bautar talala.


Duk da haka an tafi da ita, an kai ta cikin bauta. An fyaɗa ƙanananta a ƙasa, An yi kacakaca da su a kowace mararraba. An jefa kuri'a a kan manyan mutanenta, Aka ɗaure dukan manyan mutanenta da sarƙoƙi.


Wajen ƙarfe uku na dare sai Yesu ya nufo su, yana tafe a kan ruwan tekun.


Da asussuba ya tashi ya fita, ya tafi wani wuri inda ba kowa, ya yi addu'a a can.


To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne,


A kwanakin nan Yesu ya fita ya hau dutse domin yin addu'a. Dare farai yana addu'a ga Allah.


Saboda haka, a kowane wuri ina so maza su yi addu'a, suna ɗaga hannuwa tsarkakakku, ba tare da fushi ko jayayya ba.


Gidiyon da mutum ɗari da suke tare da shi, suka kai gefen sansanin wajen tsakiyar dare, bayan an sauya matsara. Sai suka busa ƙahonin, suka fasa tulunan da suke a hannuwansu.


Hannatu kuwa ta amsa ta ce, “Ba haka ba, ya shugabana, ni mace ce da take baƙin ciki ƙwarai. Ni ban sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa maye ba, amma ina faɗa wa Ubangiji dukan abin da yake a zuciyata.


Isra'ilawa fa suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa, suka zuba a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a ranan nan, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi.” Sama'ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra'ilawa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan