Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Ya Sihiyona, ki yi kuka ga Ubangiji, Bari hawayenki su gudana dare da rana kamar ruwan rafi, Kada ki huta, kada kuma idanunki su huta!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Zuciyar mutane ta yi kuka ga Ubangiji. Ya bangon Diyar Urushalima, bar hawayenki su zuba kamar rafi dare da rana; kada ki huta, kada idanunki su huta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:18
14 Iomraidhean Croise  

Hawayena suna malalowa kamar kogi, Saboda jama'a ba su biyayya da shari'arka ba.


Ina kira gare ka da zuciya ɗaya, Ka amsa mini, ya Ubangiji, Zan yi biyayya da umarnanka!


Amma idan ba za ku ji ba, Raina zai yi kuka a ɓoye saboda girmankanku, Idanuna za su yi kuka ƙwarai, za su zub da hawaye, Domin an kai garken Ubangiji zuwa bauta.


“Irmiya, ka faɗa wa mutanen baƙin ciki da ya same ka, Ka ce, ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana, Kada su daina, saboda an buge budurwa, 'yar jama'ata, An yi mata babban rauni da dūka mai tsanani.


Na ji kuka kamar na mace wadda take naƙuda, Na ji nishi kamar na mace a lokacin haihuwarta ta fari, Na ji kukan 'yar Sihiyona tana kyakyari, Tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina, gama ina suma a gaban masu kisankai!”


Da ma kaina ruwa ne kundum, Idanuna kuma maɓuɓɓuga ne, Da sai in yi ta kuka dare da rana, Saboda an kashe jama'ata!


“Ina kuka saboda waɗannan abubuwa, Hawaye suna zuba sharaf-sharaf daga idanuna. Gama mai ta'azantar da ni, Wanda zai sa in murmure yana nesa da ni. 'Ya'yana sun lalace, Gama maƙiyi ya yi nasara!”


Da dare tana kuka mai zafi, Hawaye suna zuba sharaf-sharaf a kumatunta. Dukan masoyanta ba wanda yake ta'azantar da ita. Dukan abokanta sun ci amanarta, sun zama maƙiyanta.


Ubangiji ya yi niyya Ya mai da garun Sihiyona kufai, Ya auna ta da igiyar awo, Bai janye dantsensa daga hallaka ta ba. Ya sa kagara da garu su zozaye, su lalace tare.


Ba su yi kuka gare ni da zuciya ɗaya ba, Sa'ad da suke kuka a gadajensu, Sun tsattsaga jikinsu domin abinci da ruwan inabi. Sun yi mini tawaye.


Dutse zai yi kuka daga garu, Katako kuwa zai amsa masa daga aikin da aka yi da itace.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan