Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Ubangiji ya aikata abin da ya yi niyya, Ya cika maganarsa wadda ya faɗa tun dā, Ya hallakar, ba tausayi, Ya sa maƙiyi ya yi murna a kanki, Ya ƙarfafa ƙarfin maƙiyanki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Ubangiji ya yi abin da ya shirya; ya cika maganarsa, wadda ya umarta tun daɗewa. Ya jefar da ke ba tausayi, ya bari maƙiya sun yi nasara da ke, ya ɗaukaka ƙahon maƙiyanki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:17
28 Iomraidhean Croise  

sai in raba jama'ar Isra'ila da ƙasar da na ba su, Haikalin kuma da na tsarkake domin sunana, zan kawar da shi daga gabana. Jama'ar Isra'ila kuwa za su zama abin karin magana, da abin ba'a a wurin dukan mutane.


Kai mai adalci ne, ya Ubangiji, ka shaida rashin laifina, Kada ka bar maƙiyana su ƙyaface ni, ya Allahna!


Ka sa waɗanda suka ƙyaface ni a wahalata, A rinjaye su, su ruɗe. Ka sa waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni, Su sha kunya da wulakanci!


Kada ka bar magabtana su yi murna saboda wahalata. Kada ka bar su su yi kirari a kan faɗuwata!


Ka ba maƙiyansa nasara, Ka sa dukansu su yi murna.


Ka sa makamansa su zama marasa amfani, Ka bari a ci shi da yaƙi.


Ku mutanen Filistiya, sandan da ake dūkanku da shi ya karye, amma kada wannan ya zamar muku dalilin murna. Gama idan wani maciji ya mutu, wani mafi mugunta zai maye gurbinsa. Ƙwan maciji yake ƙyanƙyashe maciji mai tashi sama!


Saboda haka yanzu, sai ka faɗa wa jama'ar Yahuza da mazaunan Urushalima, ka ce, haka Ubangiji ya faɗa, ‘Ga shi, na shirya muku masifa, ina tsara wahalar da za ta same ku. Bari kowannenku ya koma ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara al'amuransa da ayyukansa.’


“Duniya za ta yi makoki saboda wannan, Sammai za su duhunta, Gama ni na faɗa, haka kuwa na nufa in yi, Ba zan ji tausayi ba, Ba zan kuwa fāsa ba.”


Ga shi kuwa, ya yi kamar yadda ya faɗa, domin kun yi wa Ubangiji zunubi, ba ku yi biyayya da muryarsa ba, don haka wannan masifa ta auko muku.


Maƙiyanta sun zama shugabanninta, Abokan gābanta kuma sun zama iyayengijinta. Gama Ubangiji ne ya sa ta sha wahala Saboda yawan zunubanta. 'Ya'yanta sun tafi bauta wurin maƙiyanta.


Ubangiji ya yi niyya Ya mai da garun Sihiyona kufai, Ya auna ta da igiyar awo, Bai janye dantsensa daga hallaka ta ba. Ya sa kagara da garu su zozaye, su lalace tare.


“Ka yafa fushi, ka runtume mu, Kana karkashe mu ba tausayi.


Ubangiji ya saki fushinsa, Ya zuba fushinsa mai zafi. Ya kunna wa Sihiyona wuta Wadda ta cinye harsashin gininta.


“‘Tun da yake kin ƙazantar da Haikalina mai tsarki da gumakanki da abubuwanki masu banƙyama, hakika, ni Ubangiji Allah, zan kawar da ke, ba zan ji tausayinki ba, ba kuwa zan haƙura ba.


Zan yi hukunci mai zafi, ba zan yafe ba, ba kuma zan ji tausayi ba, ko da yake suna kuka da babbar murya a kunnuwana ba zan ji su ba.”


Ni kam, idona ba zai yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan sāka musu bisa ga ayyukansu.”


Ya tabbatar da maganarsa wadda ya yi a kanmu da shugabanninmu waɗanda suka yi mulkinmu. Ya aukar mana da babban bala'i, gama a duniya duka ba a taɓa yin irin abin da aka yi wa Urushalima ba.


Domin haka Ubangiji ya ce, Ga shi, yana shirya wa wannan jama'a masifa, Wadda ba za ku iya kuɓuta daga cikinta ba. Ba kuma za ku yi tafiyar alfarma ba, Gama mugun lokaci ne.


“Ni Ubangiji na ce, zan shafe dukan kome Da yake a duniya.


Amma maganata da dokokina waɗanda na umarta wa bayina annabawa, sun tabbata a kan kakanninku, sai suka tuba, suka ce, ‘Kamar yadda Ubangiji Mai Runduna ya yi niyya ya yi da mu saboda hanyoyinmu da ayyukanmu, haka kuwa ya yi da mu.’ ”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan