Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Maƙiyanki duka sun wage bakinsu gāba da ke, Suna tsāki, suna cizon bakinsu, Suna ihu, suna cewa, “Mun hallaka ta! Ai, wannan ita ce ranar da muke fata! Ga shi kuwa, ta zo, mun gan ta!”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Maƙiyanki duka suna ta surutu game da ke; suna tsaki suna cizon haƙora suna cewa, “Mun hallaka ta. Wannan ce ranar da muke jira; yau mun gan ta.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:16
31 Iomraidhean Croise  

Mugaye da maƙaryata sun tasar mini, Suna ta faɗar ƙarairayi a kaina.


Sa'ad da mugaye suka ga wannan, Sai suka tunzura, suka harare shi da fushi, suka ɓace, Sa zuciyarsu ta ƙare har abada.


Da sun haɗiye mu da rai a lokacin nan, Saboda zafin fushi da suke yi da mu,


Sun buɗe bakinsu kamar zakoki, Suna ruri, suna ta bina a guje.


Suka wahalshe ni, suka yi mini dariya, Suna hararata da ƙiyayya.


Sukan zarge ni da kakkausan harshe, Su ce, “Mun ga abin da ka yi!”


Kada ka bar su su ce wa kansu, “Madalla! Da ma abin da muke so ke nan!” Kada ka bar su su ce, “Mun rinjaye shi!”


Mugu yakan yi wa mutumin kirki makarƙashiya, Yana harararsa da ƙiyayya.


Suna cewa, “Yana ciwon ajali, Ba zai taɓa tashi daga gadonsa ba.”


Dukan yini maƙiyana suna tasar mini, Waɗanda suke faɗa da ni sun cika yawa.


Daga sammai Allah zai amsa mini, Zai kori waɗanda suka tasar mini, Allah zai nuna mini madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa.


“Aka lalatar da ƙasar, ta zama kufai, Amma yanzu za ta yi wa waɗanda suke komowa domin su zauna cikinta kaɗan. Waɗanda suka lalatar da ke kuwa, Za a kawar da su daga gare ki.


Saboda haka zan mai da wannan Haikali kamar Shilo, in mai da wannan birni ya zama abin la'ana ga dukan al'umman duniya.”


Zan fafare su da takobi, da yunwa, da masifa. Zan maishe su abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya. Za su zama abin la'ana, da abin razana, da abin raini, da abin zargi, ga dukan al'ummai, inda na kora su.


“Isra'ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne yake gaigayi ƙasusuwansu.


Duk waɗanda suka same su, sun cinye su. Maƙiyansu suka ce, ‘Ba mu yi laifi ba,’ Gama sun yi wa Ubangiji laifi, wanda yake tushen gaskiya, Ubangiji wanda kakanninsu suka dogara gare shi.


Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya cinye Urushalima, Ya ragargaza ta, Ya maishe ta kufai, Ya haɗiye ta kamar yadda dodon ruwa yakan yi, Ya cika cikinsa da kayan marmarinta, Ya tatse ta sarai.


“Sun ji yadda nake nishi, Ba mai ta'azantar da ni. Dukan maƙiyana sun ji labarin wahalar da nake ciki, Suna kuwa murna da ka yi haka. Ka kawo ranan nan da ka ambata, Domin su ma su zama kamar yadda nake.


“Dukan maƙiyanmu suna yi mana ba'a.


Ubangiji Allah ya ce, “Za ki sha babban hukuncin da 'yar'uwarki ta sha, Za a yi miki dariya da ba'a, Gama hukuncin yana da tsanani.


Ubangiji Allah ya ce, “Tun da yake Filistiyawa sun yi sakayya, sun ɗauki fansa da muguwar zuciya da ƙiyayya marar ƙarewa, don su hallakar,


Ka faɗa musu su ji maganar Ubangiji Allah.” Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun ce, ‘Madalla,’ a lokacin da aka ƙazantar da Haikalina, da lokacin da ƙasar Isra'ila ta zama kufai, da lokacin da aka kai mutanen Yahuza bautar talala,


Gama Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun tafa hannuwanku, kun buga ƙafafunku, kuka yi murna don nuna dukan ƙiyayyarku da ƙasar Isra'ila,


sai ka yi annabci ka ce, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Da yake sun maishe ku kufai marar amfani, sun kuma murƙushe ku ta kowace fuska, har kun zama abin mallakar sauran al'umma, kun zama abin magana da abin tsegumi ga mutane.


“‘Za ki zama abin zargi, da abin ba'a, da abin faɗaka, da abin tsoro ga al'ummai da suke kewaye da ke sa'ad da na hukunta ki da zarin fushina, ni Ubangiji na faɗa.


Isra'ila kamar kowace al'umma ce. Suna cikin al'ummai Kamar kaskon da ba shi da amfani,


Yanzu al'ummai sun taru suna gāba da ke, suna cewa, “Bari a ƙazantar da ita, Bari mu zura mata ido.”


Da suka ji haka, suka husata ƙwarai da gaske, har suka ciji baki don jin haushinsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan