Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Annabawanki sun gano miki wahayan ƙarya, Ba su tone asirin muguntarki, Har da za a komo da ke daga bauta ba. Amma suka yi miki annabcin ƙarya na banza.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Wahayin annabawanki ƙarya ne kuma marasa amfani; ba su tona zunubanki ba yadda za su iya ceto ki daga bauta ba. Sun yi miki annabcin ƙarya marar amfani.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:14
31 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya ce, “Ku yi kuka da ƙarfi, ba ƙaƙƙautawa! Ku ta da muryoyinku kamar busar ƙaho. Ku shaida wa jama'ata laifinsu, ku shaida wa zuriyar Yakubu zunubansu.


Firistoci kuma ba su ce, ‘Ina Ubangiji Yake’ ba? Masanan shari'a ba su san ni ba. Masu mulki sun yi mini laifi, Annabawa sun yi annabci da sunan Ba'al, Sun bi waɗansu abubuwa marasa amfani.”


Kai kuma, Fashur, da dukan waɗanda suke a gidanka, za ku tafi bauta a Babila, za ku shiga Babila, a can za ku mutu, a can za a binne ku, kai da abokanka waɗanda ka yi wa annabcin ƙarya.’ ”


Amma da a ce sun tsaya cikin shawarata, Da sun yi shelar maganata ga jama'ata, Da sun juyar da su daga muguwar hanyarsu, Da mugayen ayyukansu.


Amma ba za ku ƙara ambatar nawayar Ubangiji ba, gama maganar kowane mutum za ta zama nawaya, ga shi, kun ɓata maganar Allah mai rai, Ubangiji Mai Runduna, Allahnmu.


Sai annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka ji, ya Hananiya, Ubangiji bai aike ka ba, kana sa mutanen nan su dogara ga ƙarya.


“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce a kan Ahab ɗan Kolaya, da Zadakiya ɗan Ma'aseya, waɗanda suke yi muku annabcin ƙarya da sunana. Ga shi, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, zai kashe su a kan idonku.


Ina annabawanku waɗanda suka yi maka annabci cewa, ‘Sarkin Babila ba zai kawo wa ƙasarku yaƙi ba?’


Annabawa sun yi annabcin ƙarya, Firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, Mutanena kuwa suna so haka! Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?”


Dalili kuwa saboda zunuban annabawa ne, Da muguntar firistoci, Waɗanda suka kashe adalai.


“Kun karya zuciyar adali ta wurin ƙaryarku, ko da yake ni ban karya zuciyarsa ba. Kun ƙarfafa wa mugu gwiwa, don kada ya bar hanyarsa ta mugunta, ya tsira.


Annabawanta suna kama da zakoki masu ruri waɗanda suke yayyage ganimar da suka samu. Sun kashe mutane, sun ƙwace dukiya da abubuwa masu daraja. Sun sa mata da yawa sun rasa mazansu.


Annabawanta sun yi musu shafe da farar ƙasa, wato wahayan da suke gani, da duban da suke yi musu ƙarya ne. Suna cewa Ubangiji ne ya faɗa, alhali kuwa ni Ubangiji ban faɗa musu kome ba.


Sai Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ko ka shara'anta wa Ohola da Oholiba? To, sai ka faɗa musu mugayen ayyukansu.


Ranar hukunci ta zo, ranar ramako ta iso, Isra'ila za ta sani! An ce annabi wawa ne, Mutumin da yake da ruhu kuwa mahaukaci ne, Saboda yawan muguntarku da ƙiyayyarku.


“Idan mutum ya tashi yana iskanci, yana faɗar ƙarya, ya ce, ‘Zan yi muku wa'azi game da ruwan inabi da abin sa maye,’ To, shi ne zai zama mai wa'azin mutanen nan!


Amma ni ina cike da iko, Da Ruhun Ubangiji, Da shari'a da ƙarfin hali, Don in sanar wa Yakubu da laifinsa, Isra'ila kuma da zunubinsa.


Annabawansa sakarkari ne, maciya amana. Firistocinsa sun ƙazantar da abin da yake mai tsarki. Sun kuma keta dokoki.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan