Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Me zan ce miki? Da me zan kwatanta ki, ya Urushalima? Da me zan misalta wahalarki Don in ta'azantar da ke, ya Sihiyona? Masifar da ta same ki tana da fāɗi kamar teku, Wa zai iya warkar da ke?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Me zan ce miki? Da me zan kwatanta ki, ke Diyar Urushalima? Da me zan misalta ki, yadda zan iya yi miki ta’aziyya, Ke Budurwa Diyar Sihiyona? Ciwonki yana da zurfi kamar teku. Wane ne zai iya warkar da ke?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:13
14 Iomraidhean Croise  

Sai Dawuda ya zo Ba'al-ferazim, ya ci Filistiyawa a wurin. Sa'an nan ya ce, “Ubangiji ya huda abokan gabana a idona kamar rigyawa.” Saboda haka aka sa wa wurin suna, “Ubangiji Mai Hudawa.”


Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima ya yi maka dariya, kai Sennakerib, yana yi maka ba'a.


Ka sa ƙasar ta girgiza, ka tsaga ta. Yanzu sai ka warkar da tsaguwarta, gama tana gab da fāɗuwa!


Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima yana yi maka dariya, kai Sennakerib, yana kuma yi maka ba'a.


“Irmiya, ka faɗa wa mutanen baƙin ciki da ya same ka, Ka ce, ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana, Kada su daina, saboda an buge budurwa, 'yar jama'ata, An yi mata babban rauni da dūka mai tsanani.


“Ka ƙi Yahuza ke nan ɗungum? Ranka kuma yana jin ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu, har da ba za mu iya warkewa ba? Mun zuba ido ga samun salama, amma ba wani abin alheri da ya zo. Mun kuma sa zuciya ga warkewa, amma sai ga razana.


Ba abin sanyayawa a Gileyad ne? Ba mai magani a can ne? Me ya sa ba a warkar da jama'ata ba?


Jama'a suka ce, “Su gaggauta, su ta da murya, Su yi mana kuka da ƙarfi, Har idanunmu su cika da hawaye, Giranmu kuma su jiƙe sharaf.


“Dukanku masu wucewa, ba wani abu ba ne a gare ku? Ku duba, ku gani, ko akwai baƙin ciki irin nawa, Wanda Ubangiji ya ɗora mini, A ranar fushinsa mai zafi.


“Sa'ad da Fir'auna zai gan su, zai ta'azantu a kan rundunarsa da aka kashe da takobi. Lalle Fir'auna da dukan rundunarsa za su ta'azantu. Ni Ubangiji Allah na faɗa.


Ya tabbatar da maganarsa wadda ya yi a kanmu da shugabanninmu waɗanda suka yi mulkinmu. Ya aukar mana da babban bala'i, gama a duniya duka ba a taɓa yin irin abin da aka yi wa Urushalima ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan