Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Suna yi wa uwayensu kuka, suna cewa, “Ina abinci da ruwan inabi?” Suna suma kamar mutanen da aka yi wa rauni A titunan birnin, Suna mutuwa a ƙirjin uwayensu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Suna ce wa uwayensu, “Ina burodi da ruwan inabi?” Yayinda suke suma kamar mutanen da aka ji masu ciwo a cikin birni, sa’ad da suke mutuwa a hannuwan uwayensu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:12
9 Iomraidhean Croise  

“Yanzu zuciyata ta narke Kwanakin wahala sun same ni.


Zuciyata takan ɓaci in na tuna da abin da ya wuce, Sa'ad da nakan tafi tare da taron jama'a zuwa Haikalin Allah, Ina bishe su a jere. Taron jama'a masu farin ciki, suna raira waƙa, Suna ta da murya, suna yabon Allah.


Ya jama'ata, ku dogara ya Allah a kowane lokaci! Ku faɗa masa dukan wahalarku, Gama shi ne mafakarmu.


A kan kusurwar kowane titi Mutanenki sun rafke saboda rashin ƙarfi, Sun zama kamar barewa da tarkon maharbi ya kama. Suka ji ƙarfin fushin Allah.


Saboda haka zan ba shi matsayi mai girma, Matsayi a cikin manyan mutane masu iko. Da yardarsa ya ba da ransa Ya ɗauki rabon masu laifi. Ya maye gurbin masu zunubi da yawa, Ya kuwa sha hukuncin da ya cancanci masu zunubi. Ya yi roƙo dominsu.”


Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku. Za su ƙare 'ya'yanku mata da maza. Za su cinye garkunanku na tumaki, da na awaki, da na shanu, Za su kuma cinye 'ya'yan inabinku da na ɓaurenku. Za su hallaka biranenku masu kagara da takobi, waɗanda kuke fariya da su.


Dukan jama'arta suna nishi don neman abinci, Sun ba da kayansu masu daraja saboda abinci Don su rayu. “Ya Ubangiji ka duba, ka gani, Gama an raina ni.”


Harshen jinjiri ya liƙe a dasashinsa saboda ƙishi, 'Yan yara suna roƙon abinci, Amma ba wanda ya ba su.


Zan ƙarfafa hannun Sarkin Babila, in sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir'auna, zai yi nishi a gaban Sarkin Babila, kamar mutumin da aka yi wa raunin ajali.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan