Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Idanuna sun dushe saboda kuka, Raina yana cikin damuwa. Zuciyata ta karai saboda halakar mutanena, Gama 'yan yara da masu shan mama Sun suma a titunan birnin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Idanuna sun dushe don yawan kuka, raina na cike da baƙin ciki; zuciyata ta karaya domin mutanena sun hallaka, domin yara da jarirai suna suma a kan hanyoyi a cikin birni.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:11
26 Iomraidhean Croise  

Ya harbe ni da kibau daga kowane gefe. Kiban sun ratsa jikina sun yi mini rauni, Duk da haka bai nuna tausayi ba!


Zuciyata tana tafasa, ba ta kwanciya, Kwanakin wahala sun auko mini.


Idanuna sun gaji da zuba ido ga alkawarinka. Roƙo nake, “Sai yaushe za ka taimake ni?”


Ƙarfina ya ƙare, Ya rabu da ni kamar ruwan da ya zube ƙasa. Dukan gaɓoɓina sun guggulle, Zuciyata ta narke kamar narkakken kakin zuma.


Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, Gama ina shan wahala, Idanuna sun gaji saboda yawan kuka, Na kuwa tafke ƙwarai!


An ragargaza ni sarai, an kuwa ci nasara a kaina, Na damu a zuciyata, ina nishi don zafi.


Idanuna sun yi kumburi saboda yawan kuka, Har da ƙyar nake iya gani, Duk kuwa saboda abokan gābana!


Na gaji da kira, ina neman taimako, Maƙogwarona yana yi mini ciwo, Idanuna duka sun gaji, Saboda ina zuba ido ga taimakonka.


Ni dai ƙyale ni kurum, in yi ta kuka mai zafi. Kada ka yi ƙoƙarin ta'azantar da ni, saboda yawancin mutanena sun mutu.


Muryata ƙarama ce, ba kuma ƙarfi, Na kuwa yi kuka kamar kurciya, Idanuna sun gaji saboda duban sama. Ya Ubangiji, ka cece ni daga dukan wannan wahala.


A kan kusurwar kowane titi Mutanenki sun rafke saboda rashin ƙarfi, Sun zama kamar barewa da tarkon maharbi ya kama. Suka ji ƙarfin fushin Allah.


“Irmiya, ka faɗa wa mutanen baƙin ciki da ya same ka, Ka ce, ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana, Kada su daina, saboda an buge budurwa, 'yar jama'ata, An yi mata babban rauni da dūka mai tsanani.


Azaba! Ba zan iya daurewa da azaba ba! Zuciyata! Gabana yana faɗuwa da ƙarfi, Ba zan iya yin shiru ba, Gama na ji amon ƙaho da hargowar yaƙi.


“Yanzu, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ina tambaya, me ya sa kuke jawo wa kanku wannan babbar masifa, kuna so ku hallakar da mata da maza, yara da jarirai daga cikin Yahuza, har a rasa wanda zai wanzu?


Ku ji kukan jama'ata ko'ina a ƙasar, “Ubangiji, ba shi a Sihiyona ne? Sarkinta ba ya a cikinta ne?” Ubangiji ya ce, “Me ya sa suka tsokane ni da sassaƙaƙƙun gumakansu, Da baƙin gumakansu?”


Dukan jama'arta suna nishi don neman abinci, Sun ba da kayansu masu daraja saboda abinci Don su rayu. “Ya Ubangiji ka duba, ka gani, Gama an raina ni.”


“Ina kuka saboda waɗannan abubuwa, Hawaye suna zuba sharaf-sharaf daga idanuna. Gama mai ta'azantar da ni, Wanda zai sa in murmure yana nesa da ni. 'Ya'yana sun lalace, Gama maƙiyi ya yi nasara!”


“Ka duba, ya Ubangiji, ina shan wahala, Raina yana cikin damuwa, Zuciyata tana makyarkyata saboda tayarwata. A titi takobi yana karkashewa, A gida kuma ga mutuwa.


Saboda wannan zuciyarmu ta ɓaci, Idanunmu kuma suka duhunta.


don lokaci na zuwa da za su ce, ‘Albarka tā tabbata ga matan da suke bakararru, waɗanda ba su taɓa haihuwa ba, waɗanda kuma ba a taɓa shan mamansu ba.’


sai suka yi ta kuka da ƙarfi, har ƙarfinsu ya ƙare.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan