Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Ubangiji ya duhunta Sihiyona saboda fushinsa! Daga Sama kuma ya jefar da darajar Isra'ila a ƙasa. Bai kuma tuna da matashin sawayensa ba A ranar fushinsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Yadda Ubangiji ya rufe Diyar Sihiyona da gizagizan fushi! Ya jefar da darajar Isra’ila daga sama zuwa ƙasa; bai tuna da wurin ɗora ƙafafunsa ba a ranar fushinsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:1
28 Iomraidhean Croise  

“An kashe darajarki, ya Isra'ila, a kan tuddanki! Jarumawan sojojinmu sun fāɗi!


Sarki Dawuda fa ya miƙe tsaye, ya ce, “Ku saurare ni, ku 'yan'uwana, da jama'ata. Na yi niyya a zuciyata in gina wa akwatin alkawari na Ubangiji wurin hutawa, da wurin zaman zatin Allah. Na riga na yi shiri domin ginin,


Muka ce, “Bari mu tafi Haikalin Ubangiji, Mu yi sujada a gaban kursiyinsa!”


Ka sa shi ya tsofe kafin lokacinsa, Ka rufe shi da kunya.


Ku yabi Ubangiji Allahnmu, Ku yi sujada a gaban kursiyinsa! Mai Tsarki ne shi!


Haikalinmu, kyakkyawan keɓaɓɓen wuri inda kakanninmu suka yi yabonka, aka lalatar da shi da wuta, dukan wuraren da muka ƙauna aka lalatar da su.


Dukan masu ƙaunarku sun manta da ku, Ba su ƙara kulawa da ku, Domin na yi muku bugu irin na maƙiyi. Na yi muku horo irin na maƙiyi marar tausayi, Domin laifofinku masu girma ne, Domin zunubanku da yawa suke.


Urushalima wadda take cike da mutane a dā, Yanzu tana zaman kaɗaici! Tana zama kamar mace wadda mijinta ya rasu, Ita wadda dā ta zama babba a cikin sauran al'ummai! Ita wadda take a dā sarauniya a cikin larduna, Ta zama mai biyan gandu!


“Dukanku masu wucewa, ba wani abu ba ne a gare ku? Ku duba, ku gani, ko akwai baƙin ciki irin nawa, Wanda Ubangiji ya ɗora mini, A ranar fushinsa mai zafi.


Ubangiji ya aikata abin da ya yi niyya, Ya cika maganarsa wadda ya faɗa tun dā, Ya hallakar, ba tausayi, Ya sa maƙiyi ya yi murna a kanki, Ya ƙarfafa ƙarfin maƙiyanki.


Ƙaƙa zinariya ta zama duhu! Ƙaƙa zinariya tsantsa ta sāke! Tsarkakakkun duwatsu kuma suna zube A kowane magamin titi.


Ubangiji ya saki fushinsa, Ya zuba fushinsa mai zafi. Ya kunna wa Sihiyona wuta Wadda ta cinye harsashin gininta.


“Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce da hasalata zan sa babban hadiri mai iska, da rigyawa, da manyan ƙanƙara su hallaka shi.


Amma aka tumɓuke kurangar inabin da fushi, Aka jefar da ita ƙasa. Iskar gabas ta busar da ita, 'Ya'yanta suka kakkaɓe, Rassanta masu ƙarfi sun bushe, wuta kuwa ta cinye su.


in faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa Ubangiji Allah ya ce, ‘Zan ƙazantar da Haikalina, abin fariyarku, da abin da idanunku suke jin daɗin ganinsa, da abin faranta zuciyarku. 'Ya'yanku maza waɗanda kuka bari a baya, za a kashe su da takobi.


A Tafanes rana za ta yi duhu, Sa'ad da na karya mulkin ƙasar Masar, Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare, Za a rufe ta da gizagizai. 'Ya'yanta mata kuwa za a kai su bauta.


Za ta zama rana ce mai duhu dulum, Ranar gizagizai ce baƙi ƙirin. Runduna mai ƙarfi tana tasowa, Kamar ketowar hasken safiya bisa tsaunuka. Faufau ba a taɓa ganin irinta ba, Ba kuwa za a sāke ganin irinta ba.


Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi, har Hades. Da mu'ujizan da aka yi a cikinki, su aka yi a Saduma, da ta wanzu har ya zuwa yau.


Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi har Hades.


Sai ya ce musu, “Na ga Shaiɗan ya faɗo daga sama kamar walƙiya.


Sai ta sa wa yaron suna Ikabod, wato ɗaukaka ta rabu da Isra'ila domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma surukinta da mijinta sun rasu.


Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra'ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan