Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Urushalima ta yi zunubi ƙwarai da gaske, Saboda haka ta ƙazantu, Dukan waɗanda suka girmama ta sun raina ta Domin sun ga tsiraicinta, Ita kanta ma tana nishi, ta ba da baya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Urushalima ta yi zunubi ƙwarai saboda haka ta zama marar tsarki. Dukan masu martaba ta sun raina ta, gama sun ga tsiraicinta; ita ma da kanta tana nishi da ƙyar ta kuma juya baya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:8
33 Iomraidhean Croise  

Sai dukansu biyu idanunsu suka buɗe, sa'an nan suka gane tsirara suke, sai suka samo ganyayen ɓaure suka ɗinɗinka suka yi wa kansu sutura.


Amma idan kai, ko 'ya'yanka, kun bar bina, ba ku kiyaye umarnaina da dokokina ba, waɗanda na yi muku, amma kuka tafi, kuka bauta wa waɗansu gumaka, kuka yi musu sujada,


sai in raba jama'ar Isra'ila da ƙasar da na ba su, Haikalin kuma da na tsarkake domin sunana, zan kawar da shi daga gabana. Jama'ar Isra'ila kuwa za su zama abin karin magana, da abin ba'a a wurin dukan mutane.


Waɗansu kuwa za su amsa su ce, ‘Saboda sun bar bin Ubangiji Allahnsu wanda ya fito da kakanninsu daga ƙasar Masar, suka bi waɗansu gumaka, suka yi musu sujada, suka bauta musu, domin haka Ubangiji ya ɗora musu wannan masifa.’ ”


Mutane za su gan ki a ƙasƙance, a kunyace kuma, A tuɓe ki tsirara kamar yarinyar da take baiwa. Zan ɗauki fansa, ba kuwa wanda zai hana ni.”


Idan kun ce a zuciyarku, ‘Me ya sa waɗannan abubuwa suka same mu?’ Saboda yawan zunubanku ne, Shi ya sa an tone tsiraicinku, Aka wahalshe ku.


Ni kaina kuma zan kware muku suturarku ta rufe fuskarku Don a ga tsiraicinku.


Zan kuma sa su zama abin banƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manassa ɗan Hezekiya, Sarkin Yahuza ya aikata a Urushalima.


Zan maishe su abin ƙyama da masifa ga mulkokin duniya duka. Za su zama abin zargi, da karin magana, da ba'a, da la'ana a dukan wuraren da zan warwatsa su.


Amma sa'ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.


Domin haka ni Ubangiji na ce, ba biyayya kuka yi mini ba, da irin shelar 'yancin da kowannenku ya yi wa ɗan'uwansa da maƙwabcinsa, saboda haka ni zan yi muku shelar 'yanci zuwa mutuwa ta takobi, da annoba, da yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya.


Na ji kuka kamar na mace wadda take naƙuda, Na ji nishi kamar na mace a lokacin haihuwarta ta fari, Na ji kukan 'yar Sihiyona tana kyakyari, Tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina, gama ina suma a gaban masu kisankai!”


Su duka masu taurinkai ne, 'yan tawaye, Suna yawo suna baza jita-jita. Su tagulla ne da baƙin ƙarfe, Dukansu lalatattu ne.


Dukan jama'arta suna nishi don neman abinci, Sun ba da kayansu masu daraja saboda abinci Don su rayu. “Ya Ubangiji ka duba, ka gani, Gama an raina ni.”


Sihiyona tana miƙa hannuwanta, Amma ba wanda zai ta'azantar da ita. Gama Ubangiji ya umarci maƙwabtan Yakubu su zama maƙiyansa. Urushalima kuma ta zama ƙazantacciya a tsakaninsu.


Dattawan Sihiyona suna zaune a ƙasa shiru, Sun yi hurwa, suna saye da tufafin makoki. 'Yan matan Urushalima kuma sun sunkuyar da kansu ƙasa.


Ki yi farin ciki, ki yi murna, ke Edom, Wadda kike zaune cikin ƙasar Uz. Amma fa za a ba ki ƙoƙo ki sha, Ki bugu har ki yi tsiraici.


Za su nuna miki ƙiyayya, za su ƙwace dukiyarki su bar ki tsirara tik, za su kuma buɗe tsiraicin karuwancinki.


“Gama ni Ubangiji Allah na ce, a kawo rundunar soja ta yi yaƙi da su, don su firgita su, su washe su.


Al'ummai kuma za su sani an kai jama'ar Isra'ila zaman bautar talala saboda muguntarsu, domin sun yi mini ha'inci, ni kuwa na kawar da fuskata daga gare su, na bashe su a hannun abokan gābansu, suka ci su da yaƙi.


Yanzu zan buɗe tsiraicinta A idon samarinta, Ba kuwa wanda zai cece ta daga hannuna.


In ba haka ba, sai in yi mata tsiraici, In bar ta kamar ran da aka haife ta. In maishe ta kamar jeji, In bar ta kamar busasshiyar ƙasa, In kashe ta da ƙishi.


Saboda haka, ina yi maka shawara ka sayi zinariya a guna, wadda aka tace da wuta, don ka arzuta, da kuma fararen tufafi da za ka yi sutura, ka rufe tsiraicinka don kada ka ji kunya, da kuma man shafawa a ido don ka sami gani.


Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan