Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:7 - Littafi Mai Tsarki

7 A kwanakin wahalarta na rashin wurin zama, Urushalima ta tuna da dukan abubuwanta masu daraja a dā. A lokacin da mutanenta suka fāɗa a hannun maƙiyi, Ba wanda ya taimake ta, Maƙiyanta sun gan ta, Sun yi mata ba'a saboda fāɗuwarta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 A cikin kwanakin da take shan wahala take kuma yawo Urushalima ta tuna da dukan dukiyar da take da ita a kwanakin dā can. Sa’ad da mutanenta suka faɗa cikin hannun abokan gābanta, ba wanda ya taimake ta. Maƙiyanta suka dube ta suka yi mata dariya don hallakar da ta auko mata.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:7
23 Iomraidhean Croise  

Da ma ina cikin lokacin da ya wuce ne, Lokacin da Allah yake lura da ni,


Zuciyata takan ɓaci in na tuna da abin da ya wuce, Sa'ad da nakan tafi tare da taron jama'a zuwa Haikalin Allah, Ina bishe su a jere. Taron jama'a masu farin ciki, suna raira waƙa, Suna ta da murya, suna yabon Allah.


Lokacin da na tuna da Allah na yi ajiyar zuciya. Sa'ad da nake tunani, Nakan ji kamar in fid da zuciya.


Sauran al'ummar da take kewaye da mu, Suka maishe mu abin ba'a, suka yi mana dariya, Suka yi mana ba'a.


Keɓaɓɓun biranenka suna kama da hamada, aka kuma ƙaurace wa kufan Urushalima.


Haikalinmu, kyakkyawan keɓaɓɓen wuri inda kakanninmu suka yi yabonka, aka lalatar da shi da wuta, dukan wuraren da muka ƙauna aka lalatar da su.


“Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na ce ka faɗa wa Sarkin Yahuza wanda ya aiko ka ka tambaye ni, ka faɗa masa cewa, ‘Rundunar sojojin Fir'auna, wadda ta kawo maka gudunmawa tana gab da juyawa zuwa ƙasarta a Masar.


Kin yi wa mutanen Isra'ila dariya. A kowane lokacin da kika ambaci sunansu, sai ki taɗa kanki da raini kamar an kama su tare da ɓarayi.


Idanunmu sun gaji Da zuba ido a banza don samun taimako, Mun zuba ido Ga al'ummar da ba za ta iya cetonmu ba.


Ka faɗa musu su ji maganar Ubangiji Allah.” Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun ce, ‘Madalla,’ a lokacin da aka ƙazantar da Haikalina, da lokacin da ƙasar Isra'ila ta zama kufai, da lokacin da aka kai mutanen Yahuza bautar talala,


Gama Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun tafa hannuwanku, kun buga ƙafafunku, kuka yi murna don nuna dukan ƙiyayyarku da ƙasar Isra'ila,


Za ta bi samarinta, amma ba za ta tarar da su ba. Za ta neme su, amma ba za ta same su ba. Sa'an nan za ta ce, ‘Zan koma wurin mijina na fari, Gama zamana na dā ya fi na yanzu!’


Yanzu al'ummai sun taru suna gāba da ke, suna cewa, “Bari a ƙazantar da ita, Bari mu zura mata ido.”


Amma da ya tara hankalinsa sai ya ce, ‘Kaitona! Nawa ne daga cikin barorin ubana da suke da abinci, da yake kamar ƙasa a gare su! Ga ni a nan kuwa, yunwa tana kisana!


Amma Ibraham ya ce, ‘Ɗana, ka tuna fa, a zamanka na duniya ka sha duniyarka, Li'azaru kuwa ya sha wuya. Amma yanzu daɗi ake ba shi, kai kuwa kana shan azaba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan