Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Dukan darajar Sihiyona ta rabu da ita, Shugabanninta sun zama kamar bareyin Da ba su sami wurin kiwo ba, Suna gudu ba ƙarfi a gaban wanda yake korarsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Diyar Sihiyona ba ta da sauran daraja. ’Ya’yan sarakunanta sun zama kamar bareyi waɗanda suka rasa wurin kiwo; cikin rashin ƙarfi suka guje wa masu fafararsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:6
31 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima ya yi maka dariya, kai Sennakerib, yana yi maka ba'a.


Sai aka huda garun birnin, sarki da mayaƙa suka tsere da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu kusa da gonar sarki, suka bi ta hanyar Araba, ko da yake Kaldiyawa suna kewaye da birnin.


Amma sojojin Kaldiyawa suka runtumi sarki suka kamo shi a filayen Yariko. Sojojinsa duka suka watse, suka bar shi.


Allah yana haskakawa daga Sihiyona, Da cikar jamalin Sihiyona.


Ku durƙusa a gaban Mai Tsarki, sa'ad da ya bayyana, Ku yi rawar jiki a gabansa, ku duniya duka!


Birnin da yake dā mai aminci ne, yanzu ya zama kamar karuwa! Dā adalai a can suke zaune, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai.


Bari dukan waɗanda suke zaune a Sihiyona su yi sowa su raira waƙa! Gama Mai Tsarki, Allah na Isra'ila, mai girma ne, Yana zaune tare da mutanensa.”


Sa'an nan a kan Dutsen Sihiyona, da a kan dukan waɗanda suka tattaru a can, Ubangiji zai aika da girgije da rana, hayaƙi da hasken harshen wuta kuma da dare. Darajar Ubangiji za ta rufe, ta kuma kiyaye birnin duka.


Ubangiji ya ce wa Irmiya, “Ka faɗa wa sarki da sarauniya, uwarsa, su sauka daga gadon sarautarsu, Domin an tuɓe kyakkyawan rawanin sarautarsu daga kansu.


“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce wa dukan waɗanda aka kai bauta, wato waɗanda ya aika da su bauta daga Urushalima zuwa Babila.


Da jin takawar kofatan dawakai, Da amon karusai da ƙafafun karusai, Ubanni ba su juya, su dubi 'ya'yansu ba, Domin hannuwansu sun yi laƙwas,


Za a ci garuruwa da kagarai da yaƙi, A wannan rana zukatan sojojin Mowab Za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.


Sa'an nan ya ƙwaƙule idanun Zadakiya, ya kuma sa masa ƙuƙumi, aka kai shi Babila inda aka sa shi a kurkuku har ran da ya mutu.


Sai ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan manyan gidajen da suke Urushalima.


in faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa Ubangiji Allah ya ce, ‘Zan ƙazantar da Haikalina, abin fariyarku, da abin da idanunku suke jin daɗin ganinsa, da abin faranta zuciyarku. 'Ya'yanku maza waɗanda kuka bari a baya, za a kashe su da takobi.


“Kai ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu madogararsu, da murnarsu, da darajarsu, da abin da idanunsu suka ji daɗin gani, da abin da yake faranta zuciyarsu, da 'ya'yansu mata da maza,


“Ubangiji zai sa abokan gabanku su rinjaye ku cikin yaƙi. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya.


Ƙaƙa mutum ɗaya zai runtumi dubu, Mutum biyu kuma su kori zambar goma, Sai dai Dutsensu ya sayar da su, Ubangiji kuma ya bashe su?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan