Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Maƙiyanta sun zama shugabanninta, Abokan gābanta kuma sun zama iyayengijinta. Gama Ubangiji ne ya sa ta sha wahala Saboda yawan zunubanta. 'Ya'yanta sun tafi bauta wurin maƙiyanta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Maƙiyanta sun zama shugabanninta; Abokan gābanta suna da kwanciyar rai. Ubangiji ya kawo mata ɓacin rai domin yawan zunubanta. ’Ya’yanta sun tafi bauta, a ƙarƙashin maƙiyanta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:5
38 Iomraidhean Croise  

saboda sun aikata mugunta a gabana, suka tsokane ni in yi fushi tun ranar da kakanninsu suka fito daga Masar har wa yau.”


Ka bar al'umman da take makwabtaka da mu Su yi ta faɗa a kan ƙasarmu, Abokan gābanmu kuma suna yi mana ba'a.


Ka ba maƙiyansa nasara, Ka sa dukansu su yi murna.


Wannan shi ne lokacin gigicewa, da shan ɗibga, da ruɗewa a cikin kwarin wahayi, Ubangiji Allah Mai Runduna shi ya aukar mana da shi. An ragargaza garukan birninmu har ƙasa, ana jin amsar kuwwar koke-kokenmu na neman taimako a cikin tsaunuka.


Abokan gabanmu sun kusa su kori mutanenka gaba ɗaya sun kuma tattake Haikalinka.


An lalatar da alfarwata, Dukan igiyoyi sun tsintsinke, 'Ya'yana maza sun bar ni, ba su nan. Ba wanda zai kafa mini alfarwata Ya kuma rataya labulena.


Ubangiji ya ce, “Na bar jama'ata. Na rabu da gādona, Na ba da wanda raina yake ƙauna a hannun maƙiyansa.


Amma cikin annabawa na Urushalima, Na ga abin banƙyama. Suna yin zina, suna ƙarya, Suna ƙarfafa hannuwan masu aikata mugunta, Saboda haka ba wanda ya juya ga barin muguntarsa, Dukansu suna kama da Saduma, Mazaunanta kuwa kamar Gwamrata.”


Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashi sauran mutane da suka ragu a birnin zuwa babila, wato mutanen da suka gudu zuwa wurinsa.


“Ba zan hukunta su saboda waɗannan abubuwa ba? Ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kan al'umma irin wannan ba?


“Ina kuka saboda waɗannan abubuwa, Hawaye suna zuba sharaf-sharaf daga idanuna. Gama mai ta'azantar da ni, Wanda zai sa in murmure yana nesa da ni. 'Ya'yana sun lalace, Gama maƙiyi ya yi nasara!”


“Abin da Ubangiji ya yi daidai ne, Gama ni na ƙi bin maganarsa, Ku ji, ya ku jama'a duka, Ku dubi wahalata, 'Yan matana da samarina, An kai su bauta!


Urushalima ta yi zunubi ƙwarai da gaske, Saboda haka ta ƙazantu, Dukan waɗanda suka girmama ta sun raina ta Domin sun ga tsiraicinta, Ita kanta ma tana nishi, ta ba da baya.


Ubangiji ya aikata abin da ya yi niyya, Ya cika maganarsa wadda ya faɗa tun dā, Ya hallakar, ba tausayi, Ya sa maƙiyi ya yi murna a kanki, Ya ƙarfafa ƙarfin maƙiyanki.


“Dukan maƙiyanmu suna yi mana ba'a.


Ni kam, idona ba zai yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan sāka musu bisa ga ayyukansu.”


Sa'an nan ya ce mini, “Zunubin mutanen Isra'ila da Yahuza ya kasaita ƙwarai. Ƙasar tana cike da jini, birnin kuma yana cike da rashin imani, gama sun ce, ‘Ubangiji ya rabu da ƙasar, ba ya ganinmu.’


Gama na sani bayan rasuwata za ku aikata mugunta, ku kauce daga hanyar da na umarce ku. Masifa za ta auko muku a kwanaki masu zuwa saboda za ku aikata mugunta a gaban Ubangiji, za ku tsokani fushinsa da aikin hannuwanku.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan