Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Hanyoyin Sihiyona suna baƙin ciki Domin ba mai halartar ƙayyadaddun idodi. Dukan ƙofofinta sun zama kufai, Firistocinta suna nishi, Budurwanta kuma suna wahala, Ita kanta ma tana shan wuya ƙwarai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Hanyoyin zuwa Sihiyona suna makoki, gama ba wanda ya zo bikin da ta shirya. Ba kowa a hanyoyin shiganta. Firistocinta suna gurnani, ’yan matana kuma suna wahala, kuma tana cikin shan wahala ƙwarai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:4
19 Iomraidhean Croise  

Ƙofofin birnin za su yi makoki, su yi kuka. Za a kamanta birnin da matar da take zaune a ƙasa tsirara.


Ku ji fa, an ji ƙishin-ƙishin! Ga shi kuma, yana tafe. Akwai babban hargitsin da ya fito daga arewa, Don a mai da biranen Yahuza kufai, wurin zaman diloli.


“Yahuza tana makoki, Ƙofofin biranenta suna lalacewa, Mutanenta suna kwance a ƙasa, suna makoki, Urushalima tana kuka da babbar murya.


“Ni Ubangiji na ce, zan mai da Urushalima tsibin kufai, Wurin zaman diloli, Zan kuma mai da biranen Yahuza kufai, inda ba kowa.”


“Sun ji yadda nake nishi, Ba mai ta'azantar da ni. Dukan maƙiyana sun ji labarin wahalar da nake ciki, Suna kuwa murna da ka yi haka. Ka kawo ranan nan da ka ambata, Domin su ma su zama kamar yadda nake.


An tilasta wa samari su yi niƙa, Yara kuma suna tagataga da kayan itace.


Tsofaffi sun daina zama a dandalin ƙofar birni, Samari kuma sun daina bushe-bushe.


Zan hukunta ta saboda kwanakin idodin gunkin nan Ba'al. A kwanakin nan takan ƙona musu turare, Ta yi ado da zobe da lu'ulu'ai, Ta bi samarinta, amma ta manta da ni.” In ji Ubangiji.


Zan kuwa turo muku mugayen namomin jeji waɗanda za su kashe 'ya'yanku, su hallakar da dabbobinku, su sa ku zama kaɗan, har ba mai gilmayya a hanyoyinku.


Saboda ku kuwa za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin kufai, Dutse inda Haikali yake zai zama kurmi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan