Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Yahuza ta tafi bauta tana shan azaba, Da bauta mai tsanani. Tana zaune a tsakiyar sauran al'umma, Amma ba ta sami hutawa ba, Gama masu runtumarta sun ci mata, ba hanyar tsira.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Bayan wahala da baƙin ciki, Yahuda ta tafi bauta. Ta zauna a cikin ƙasashe, ba tă samu wurin hutawa ba. Duk masu fafararta sun same ta sa’ad da take cikin matuƙar ɓacin rai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:3
22 Iomraidhean Croise  

Sai Nebuzaradan shugaban sojojin, ya kwashe sauran mutanen da suka ragu a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran da suka ragu, ya kwashe ya kai su zaman talala.


Sarkin Babila kuwa ya kashe su a can. Haka aka kai mutanen Yahuza zuwa zaman talala.


Sai aka huda garun birnin, sarki da mayaƙa suka tsere da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu kusa da gonar sarki, suka bi ta hanyar Araba, ko da yake Kaldiyawa suna kewaye da birnin.


Amma sojojin Kaldiyawa suka runtumi sarki suka kamo shi a filayen Yariko. Sojojinsa duka suka watse, suka bar shi.


An kulle biranen Negeb, Ba wanda zai buɗe su, Yahuza duka an kai ta zaman dole, Dukanta an kai ta zaman dole.


“Ga shi, ina aiko da masunta da yawa,” in ji Ubangiji, “za su kuwa kama su, daga baya kuma zan aika da mafarauta da yawa, za su farauce su daga kowane tsauni, da tudu, da kogwannin duwatsu.


Zan maishe su abin ƙyama da masifa ga mulkokin duniya duka. Za su zama abin zargi, da karin magana, da ba'a, da la'ana a dukan wuraren da zan warwatsa su.


Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashi sauran mutane da suka ragu a birnin zuwa babila, wato mutanen da suka gudu zuwa wurinsa.


Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran masu sana'a, ya kai su bautar talala a Babila.


Amma sojojin Kaldiyawa suka runtumi sarki Zadakiya, suka ci masa a filayen Yariko. Dukan sojoji suka yashe shi.


Ƙofofinta sun nutse ƙasa, Ya lalatar, ya kakkarya ƙyamarenta, An kai sarkinta da mahukuntanta cikin al'ummai, Inda ba a bin dokokin annabawanta, Ba su kuma samun wahayi daga wurin Ubangiji.


Mutane suka yi ta yi musu ihu, Suna cewa, “Ku tafi, ku ƙazamai, Ku tafi, ku tafi, kada ku taɓa mu!” Don haka suka zama korarru, masu kai da kawowa. A cikin sauran al'umma mutane suna cewa, “Ba za su ƙara zama tare da mu ba.”


Masu binmu a ƙyeyarmu suke, suna korarmu da zafi, Mun gaji, ba a yarda mu huta.


Sulusinki zai mutu da annoba da yunwa. Takobi kuma zai kashe sulusinki, sa'an nan zan watsar da sulusinki ko'ina, zan kuma zare takobi a kansu.


domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan