Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:22 - Littafi Mai Tsarki

22 “Ka sa mugayen ayyukansu su bayyana a gabanka, Sa'an nan ka hukunta su kamar yadda ka hukunta ni saboda dukan laifofina. Gama nishe-nishena sun yi yawa. Zuciyata kuma ta karai.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 “Bari ka ga muguntarsu duka; ka yi musu yadda ka yi mini domin dukan zunubansu. Nishina da yawa kuma zuciyata ta gaji.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:22
16 Iomraidhean Croise  

Yanzu ka amsa mini, ya Ubangiji! Na fid da zuciya duka! Kada ka ɓuya mini, Don kada in zama cikin waɗanda suke gangarawa zuwa lahira.


Don me al'ummai za su tambaye mu cewa, “Ina Allahnku?” Bari mu ga ka hukunta al'ummai Saboda sun zubar da jinin bayinka!


Hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa.


Ka kwarara hasalarka a kan sauran al'umma da ba su san ka ba, Da a kan jama'ar da ba su kiran sunanka, Gama sun cinye Yakubu, Sun cinye shi, sun haɗiye shi, Sun kuma mai da wurin zamansa kufai.”


Amma ya Ubangiji, Ka san dukan maƙarƙashiyarsu, su kashe ni, Kada ka gafarta musu muguntarsu, kada kuma ka shafe zunubinsu daga gabanka. Ka sa a jefar da su daga gabanka, Ka yi da su sa'ad da kake fushi!”


Domin haka dukan waɗanda suka cinye ku, za a cinye su, Dukan maƙiyanku, kowane ɗayansu zai tafi bauta, Waɗanda suka washe ku, za a washe su. Dukan waɗanda suka kwashe ku ganima, su ma za a kwashe su ganima.


Bari mutanen Sihiyona su ce, “Allah ya sa muguntar da mutanen Babila suka yi mana ta koma kansu!” Bari kuma mutanen Urushalima su ce, “Allah ya sa hakkin jininmu ya koma kan Kaldiyawa!”


Baƙin cikina ya fi ƙarfin warkewa, Zuciyata ta ɓaci ƙwarai!


“Daga sama ya aukar da wuta a cikin ƙasusuwana. Ya kuma kafa wa ƙafafuna ashibta, Ya komar da ni baya, Ya bar ni a yashe, sumamme dukan yini.


Saboda wannan zuciyarmu ta ɓaci, Idanunmu kuma suka duhunta.


In fa irin abubuwan nan suna faruwa ga ɗanye, yaya zai zama ga ƙeƙasasshe?”


Saboda haka, ina roƙonku kada ku karai da ganin wahalar da nake sha dominku, wannan kuwa ɗaukakarku ce.


Sai suka ta da murya da ƙarfi suka ce, “Ya Ubangiji Mamallaki, Mai Tsarki, Mai Gaskiya, sai yaushe ne za ka yi hukunci, ka ɗaukar mana fansar jininmu a gun mazaunan duniya?”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan