Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Da dare tana kuka mai zafi, Hawaye suna zuba sharaf-sharaf a kumatunta. Dukan masoyanta ba wanda yake ta'azantar da ita. Dukan abokanta sun ci amanarta, sun zama maƙiyanta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Tana yin kuka mai zafi da dare, hawaye na gangara a kan kumatunta. A cikin masoyanta duka babu wanda ya yi mata ta’aziyya. Duk abokanta sun yashe ta; sun zama abokan gābanta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:2
30 Iomraidhean Croise  

Amma ku abokaina, kun ruɗe ni, Kamar rafi wanda yakan ƙafe da rani.


Wata da watanni ina ta aikin banza, Kowane dare ɓacin rai yake kawo mini.


Ka sa waɗanda suke kuka a lokacin da suke dashe, Su tattara albarkar kaka da farin ciki!


Magabtana duka suna mini ba'a, Maƙwabtana sun raina ni, Waɗanda suka san ni kuwa suna jin tsorona, Sa'ad da suka gan ni a kan titi sukan guje mini.


Na gaji tiƙis saboda baƙin ciki, Kowane dare gadona yakan jiƙe saboda kukana. Matashin kaina ya yi sharkaf da hawaye.


Sa'ad da na ji yunwa, sai suka ba ni dafi, Sa'ad da na ji ƙishi, sai suka ba ni ruwan tsami.


'Yan'uwan matalauci ba su bukatarsa, ba abin mamaki ba ne ya rasa abokai. Kome ƙoƙarin da zai yi ba zai sami ko ɗaya ba.


Amma idan ba za ku ji ba, Raina zai yi kuka a ɓoye saboda girmankanku, Idanuna za su yi kuka ƙwarai, za su zub da hawaye, Domin an kai garken Ubangiji zuwa bauta.


Kai Isra'ila, kada ka bar ƙafafunka ba takalma, Kada kuma ka bar maƙogwaronka ya bushe. Amma ka ce, ‘Wannan ba amfani, Gama na ƙaunaci baƙi, su kuwa zan bi.’


Ubangiji ya ce, “Idan mutum ya saki matarsa, Ta kuwa rabu da shi, har ta auri wani, Ya iya ya komo da ita? Ashe, yin haka ba zai ƙazantar da ƙasar ba? Ya Isra'ila, kin yi karuwanci, Abokan sha'anin karuwancinki, suna da yawa. Za ki sāke komowa wurina? Ni, Ubangiji, na faɗa.


Dukan masu ƙaunarku sun manta da ku, Ba su ƙara kulawa da ku, Domin na yi muku bugu irin na maƙiyi. Na yi muku horo irin na maƙiyi marar tausayi, Domin laifofinku masu girma ne, Domin zunubanku da yawa suke.


Ya ke da kike kufai marar kowa, Me kike nufi da kika ci ado da mulufi, Kike caɓa ado da kayan zinariya, Kika sa wa idanunki tozali ram? Kin yi kwalliyarki a banza, Abokan sha'anin karuwancinki sun raina ki, Ranki suke nema.


Da ma kaina ruwa ne kundum, Idanuna kuma maɓuɓɓuga ne, Da sai in yi ta kuka dare da rana, Saboda an kashe jama'ata!


“Na kira masoyana, amma suka yaudare ni, Firistocina da dattawana a cikin birni sun hallaka Saboda neman abincin da za su ci su rayu.


“Sun ji yadda nake nishi, Ba mai ta'azantar da ni. Dukan maƙiyana sun ji labarin wahalar da nake ciki, Suna kuwa murna da ka yi haka. Ka kawo ranan nan da ka ambata, Domin su ma su zama kamar yadda nake.


Ƙazantarta tana cikin tufafinta, Ba ta tuna da ƙarshenta ba, Domin haka faɗuwarta abar tsoro ce, Ba ta da mai yi mata ta'aziyya. “Ya Ubangiji, ka dubi wahalata, Gama maƙiyi ya ɗaukaka kansa!”


Idanuna sun dushe saboda kuka, Raina yana cikin damuwa. Zuciyata ta karai saboda halakar mutanena, Gama 'yan yara da masu shan mama Sun suma a titunan birnin.


domin haka zan tattara miki daga kowane waje dukan kwartayenki, waɗanda kika yi nishaɗi da su, wato dukan waɗanda kika ƙaunace su, da waɗanda kika ƙi. Zan sa su yi gāba da ke. Zan buɗe musu tsiraicinki don su gani.


Za ta bi samarinta, amma ba za ta tarar da su ba. Za ta neme su, amma ba za ta same su ba. Sa'an nan za ta ce, ‘Zan koma wurin mijina na fari, Gama zamana na dā ya fi na yanzu!’


Kada ka dogara ga maƙwabcinka, Kada kuma ka amince da abokinka. Ka kuma kame bakinka daga matarka Wadda take kwance tare da kai.


Waɗannan ra'ayinsu ɗaya ne, za su kuma bai wa dabbar nan ikonsu da sarautarsu.


Ƙahonin nan goma kuma da ka gani, wato, su da dabbar nan za su ƙi karuwar, su washe ta, su tsiraita ta, su ci namanta, su ƙone ta,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan