Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:18 - Littafi Mai Tsarki

18 “Abin da Ubangiji ya yi daidai ne, Gama ni na ƙi bin maganarsa, Ku ji, ya ku jama'a duka, Ku dubi wahalata, 'Yan matana da samarina, An kai su bauta!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 “Ubangiji mai adalci ne, duk da haka na yi tawaye da umarninsa. Ku saurara, jama’a duka; ku dubi wahalar da nake sha. Samarina da ’yan matana duka sun tafi bauta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:18
38 Iomraidhean Croise  

sai ya kira annabin Allah, wanda ya zo daga Yahuza, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ba ka yi biyayya da maganar Ubangiji ba, ba ka kuma kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba,


Bayan wannan dukan abubuwan nan suka same mu saboda mugayen ayyukanmu da zunubanmu masu yawa. Ya Allahnmu, ga shi ma, ka hukunta mu kaɗan bisa ga yawan zunubanmu, ka kuma bar mana wannan ringi.


“Amma suka yi maka rashin biyayya, suka tayar maka, Suka juya wa dokokinka baya, Suka karkashe anna bawan da suka faɗakar da su, Waɗanda suka faɗa musu su juyo gare ka. Suka yi ta saɓa maka lokaci lokaci.


Ka yi daidai da ka hukunta mu haka! Kai mai aminci ne, mu kuwa mun yi zunubi.


Saboda sun tayar, sun ƙi bin umarnan Allah Maɗaukaki, Sun kuwa ƙi koyarwarsa.


Kai mai adalci ne, ya Ubangiji, Dokokinka kuma daidai ne,


Na sani ka'idodinka na adalci ne, ya Ubangiji, Ka hore ni, domin kai mai aminci ne.


Ubangiji mai adalci ne a abin da yake yi duka, Mai jinƙai ne a ayyukansa duka.


Fir'auna ya aika, aka kirawo Musa da Haruna, ya ce musu, “Lalle a wannan karo na yi laifi, Ubangiji shi ne da gaskiya. Ni da jama'ata muke da kuskure.


Ya Ubangiji, kai adali ne sa'ad da na kawo ƙara a gare ka. Duk da haka zan bayyana ƙarata a gabanka, Me ya sa mugaye suke arziki cikin harkarsu? Me ya sa dukan maciya amana suke zaman lafiya, Suna kuwa ci gaba?


Amma sa'ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.


Za su kewaye Yahuza kamar masu tsaron saura, Saboda ta tayar wa Ubangiji.’ Ni Ubangiji na faɗa.


Ubangiji ya ce, “Ga shi, waɗanda ba a shara'anta su ga shan ƙoƙon hukunci ba, za su sha shi, to, kai za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, amma lalle za ka sha shi!


“Dukanku masu wucewa, ba wani abu ba ne a gare ku? Ku duba, ku gani, ko akwai baƙin ciki irin nawa, Wanda Ubangiji ya ɗora mini, A ranar fushinsa mai zafi.


“Mun yi zunubi, mun tayar, Kai kuwa ba ka gafarta ba.


Rawani ya fāɗi daga kanmu, Tamu tu ƙare, gama mun yi zunubi!


“Mun yi zunubi, mun yi laifi, mun aikata mugunta, mun yi tawaye. Mun kauce daga bin umarnanka da ka'idodinka.


Ya Ubangiji, kai mai adalci ne, amma mu sai kunya, kamar yadda yake a yau ga mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima da dukan Isra'ilawa, waɗanda suke kusa da waɗanda suke nesa a dukan ƙasashen da ka kora su saboda rashin amincin da suka yi maka.


A ranan nan kyawawan 'yan mata da samari Za su faɗi saboda ƙishirwa.


Ubangiji wanda yake cikinsa mai adalci ne, Ba ya kuskure. Yakan nuna adalcinsa kowace safiya, Kowace safiya kuwa bai taɓa fāsawa ba. Amma mugu bai san kunya ba.


Amma maganata da dokokina waɗanda na umarta wa bayina annabawa, sun tabbata a kan kakanninku, sai suka tuba, suka ce, ‘Kamar yadda Ubangiji Mai Runduna ya yi niyya ya yi da mu saboda hanyoyinmu da ayyukanmu, haka kuwa ya yi da mu.’ ”


Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nema wa kanka fushin Allah a ranar fushi, sa'ad da za a bayyana hukuncin Allah macancani.


To, mun sani duk abin da Shari'a ta ce, ya shafi waɗanda suke ƙarƙashinta ne, don a tuƙe hanzarin kowa, duk duniya kuma tă sani ƙarƙashin hukuncin Allah take.


“Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne, Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne. Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi, Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.


Ya kuma ce, “Sarakuna saba'in waɗanda aka yanyanke manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, suka kalaci abincinsu a ƙarƙashin teburina. Allah kuwa ya yi mini kamar yadda na yi musu.” Suka kawo shi Urushalima, a nan ya mutu.


Gama tayarwa kamar zunubin bokanci take. Taurinkai kuma kamar bautar gumaka yake. Kamar yadda ka ƙi umarnin Ubangiji, haka nan shi ma ya ƙi ka da zama sarki.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan