Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Sihiyona tana miƙa hannuwanta, Amma ba wanda zai ta'azantar da ita. Gama Ubangiji ya umarci maƙwabtan Yakubu su zama maƙiyansa. Urushalima kuma ta zama ƙazantacciya a tsakaninsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Sihiyona ta miƙa hannunta, amma ba wani da zai yi mata ta’aziyya. Ubangiji ya umarta cewa maƙwabtansa za su zama maƙiyansa; Urushalima ta zama abar ƙyama a cikinsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:17
29 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan Sulemanu ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron jama'ar Isra'ila. Ya ɗaga hannuwansa sama,


sai ka kasa kunne ga addu'arsu. Idan ɗaya daga cikin jama'arka Isra'ila ya matsu a zuciyarsa, ya ɗaga hannuwansa sama yana addu'a wajen wannan Haikali,


A shekara ta tara ta sarautar Zadakiya a kan rana ta goma ga watan goma, sai Nebukadnezzar Sarkin Babila, tare da sojojinsa, ya kawo wa Urushalima yaƙi. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina mata kagarai.


Sa'an nan na sāke dubawa a kan rashin adalcin da yake ci gaba a duniyan nan. Waɗanda ake zalunta suna kuka, ba kuwa wanda zai taimake su, domin waɗanda suke zaluntarsu suke da iko.


“Sa'ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu'a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu'ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku.


Ubangiji ya ce, “Ya Urushalima, mai shan wahala, birnin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi, Ba ki da wanda zai ta'azantar da ke. Zan sake gina harsashinki da duwatsu masu daraja.


Ashe, abin gadon nan nawa ya zama dabbare-dabbaren tsuntsun nan ne mai cin nama? Tsuntsaye masu cin nama sun kewaye shi? Tafi, ka tattaro namomin jeji, Ka kawo su su ci.


“Wa zai ji tausayinki, ya Urushalima? Wa zai yi baƙin ciki dominki? Wa kuma zai ratso wurinki don ya tambayi lafiyarki?


Yaro da babba za su mutu a wannan ƙasa, ba za a binne su ba, ba kuwa za a yi baƙin ciki dominsu ba. Ba kuwa wanda zai tsaga jikinsa ko ya aske kansa ƙwal dominsu.


Ni Ubangiji zan umarce su su komo zuwa wannan birni don su yi yaƙi da shi, su ci shi, su ƙone shi da wuta. Zan sa biranen Yahuza su zama kufai, ba masu zama a ciki.”


Na ji kuka kamar na mace wadda take naƙuda, Na ji nishi kamar na mace a lokacin haihuwarta ta fari, Na ji kukan 'yar Sihiyona tana kyakyari, Tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina, gama ina suma a gaban masu kisankai!”


Makiyaya da garkunansu za su zo wurinki, Za su kafa alfarwansu kewaye da ke, Kowa zai yi kiwo a makiyayarki.


Baƙin cikina ya fi ƙarfin warkewa, Zuciyata ta ɓaci ƙwarai!


“Ina kuka saboda waɗannan abubuwa, Hawaye suna zuba sharaf-sharaf daga idanuna. Gama mai ta'azantar da ni, Wanda zai sa in murmure yana nesa da ni. 'Ya'yana sun lalace, Gama maƙiyi ya yi nasara!”


“Na kira masoyana, amma suka yaudare ni, Firistocina da dattawana a cikin birni sun hallaka Saboda neman abincin da za su ci su rayu.


Da dare tana kuka mai zafi, Hawaye suna zuba sharaf-sharaf a kumatunta. Dukan masoyanta ba wanda yake ta'azantar da ita. Dukan abokanta sun ci amanarta, sun zama maƙiyanta.


“Sun ji yadda nake nishi, Ba mai ta'azantar da ni. Dukan maƙiyana sun ji labarin wahalar da nake ciki, Suna kuwa murna da ka yi haka. Ka kawo ranan nan da ka ambata, Domin su ma su zama kamar yadda nake.


Urushalima ta yi zunubi ƙwarai da gaske, Saboda haka ta ƙazantu, Dukan waɗanda suka girmama ta sun raina ta Domin sun ga tsiraicinta, Ita kanta ma tana nishi, ta ba da baya.


Ƙazantarta tana cikin tufafinta, Ba ta tuna da ƙarshenta ba, Domin haka faɗuwarta abar tsoro ce, Ba ta da mai yi mata ta'aziyya. “Ya Ubangiji, ka dubi wahalata, Gama maƙiyi ya ɗaukaka kansa!”


Mutane suka yi ta yi musu ihu, Suna cewa, “Ku tafi, ku ƙazamai, Ku tafi, ku tafi, kada ku taɓa mu!” Don haka suka zama korarru, masu kai da kawowa. A cikin sauran al'umma mutane suna cewa, “Ba za su ƙara zama tare da mu ba.”


“Ɗan mutum, sa'ad da mutanen Isra'ila suka zauna a ƙasar kansu, sun ƙazantar da ita ta wurin hanyoyinsu da ayyukansu. Halinsu a gare ni ya zama kamar rashin tsarkin mace a lokacin hailarta.


Isra'ila kamar kowace al'umma ce. Suna cikin al'ummai Kamar kaskon da ba shi da amfani,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan