Makoki 1:15 - Littafi Mai Tsarki15 “Ubangiji ya yi watsi da majiya ƙarfina, Ya kirawo taron jama'a a kaina Don su murƙushe samarina. Ya kuma tattake Urushalima, zaɓaɓɓiyarsa, Kamar 'ya'yan inabi a wurin matsewa. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202015 “Ubangiji ya ƙi duk mayaƙan da suke tare da ni; ya sa wata runduna ta tayar mini ta kuma tattake samarina. Ubangiji ya tattake budurwa Diyar Yahuda kamar ’ya’yan inabi a wurin matsewa. Faic an caibideil |
Don haka ina cike da fushin Ubangiji Na gaji da kannewa. Ubangiji ya ce, “Zan kwararo fushi kan yara da suke a titi. Da kuma kan tattaruwar samari. Za a ɗauke mata da miji duka biyu, Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufa tukub-tukub. Za a ba waɗansu gidajensu, da gonakinsu, da matansu, Gama zan nuna ikona in hukunta mazaunan ƙasar.