Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:14 - Littafi Mai Tsarki

14 “Ubangiji ya tattara laifofina Ya yi karkiya da su, Ya ɗaura su a wuyana, Ya sa ƙarfina ya kāsa. Ya kuma bashe ni a hannun Waɗanda ban iya kome da su ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 “Ya ɗaura zunubaina a wuyana; aka naɗe su a hannuwansa. Aka rataye su a wuyana Ubangiji ya kwashe ƙarfina. Ya bashe ni ga waɗanda suka fi ni ƙarfi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:14
21 Iomraidhean Croise  

Zunuban mutum tarko ne, komar zunubinsa ce take kama shi.


Zan hallaka Assuriyawa a ƙasata ta Isra'ila, in tattake su a kan duwatsuna. Zan 'yantar da jama'ata daga karkiyar Assuriyawa, daga nauyin da suka tilasta musu su ɗauka.


Na yi fushi da mutanena, Na maishe su kamar su ba nawa ba ne. Na sa su a ƙarƙashin ikonki, Ba ki kuwa yi musu jinƙai ba, Har da tsofaffi ma kin ba su wuya.


zan aiko kabilai daga arewa da bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Zan kawo su, su yi yaƙi da ƙasan nan da mazaunanta, da dukan al'umman da take kewaya da ita. Zan hallaka su sarai, in sa su zama abin ƙyama, da abin raini, da abin zargi har abada.


Sai na faɗa wa Zadakiya Sarkin Yahuza wannan magana cewa, “Ka ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanka, ka bauta masa, shi da mutanensa, don ka rayu!


“ ‘Amma idan wata al'umma ko wani mulki bai yarda ya bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila ba, bai kuma ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyansa ba, zan hukunta wa wannan al'umma da takobi, da yunwa, da annoba, har in hallaka ta, ta hannun Nebukadnezzar, ni Ubangiji na faɗa.


ya tafi ya faɗa wa Hananiya, ya ce, “Haka Ubangiji ya ce, ‘Ka karya karkiya ta itace, amma zan yi karkiya ta ƙarfe a maimakonta.


Gama haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na faɗa. Na sa wa wuyan dukan waɗannan al'ummai karkiya ta ƙarfe, don su bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila, za su kuwa bauta masa, gama na ba shi su, har da namomin jeji.’ ”


Zadakiya Sarkin Yahuza, ya sa shi a kurkuku, gama ya ce, “Don me kake yin annabci? Ka ce, Ubangiji ya ce, ga shi, zai ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa cinye shi da yaƙi.


Sarkin Babila kuwa zai tafi da Zadakiya zuwa Babila. Zai zauna can sai lokacin da na ziyarce shi. Ko da ya yi yaƙi da Kaldiyawa ba zai yi nasara ba.”


Sarki Zadakiya ya aika a kawo masa Irmiya. Sarki kuwa ya shigar da shi gidansa, ya tambaye shi a asirce, ya ce, “Ko akwai wata magana daga wurin Ubangiji?” Sai Irmiya ya ce, “Akwai kuwa!” Ya ci gaba ya ce, “Za a ba da kai a hannun Sarkin Babila.”


‘Zan fitar da ku daga cikin birnin, in bashe ku a hannun baƙi, zan hukunta ku.


Zan zubo maka da fushina, in hura maka wutar fushina. Zan bashe ka a hannun mugaye, gwanayen hallakarwa.


“Gama ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ga shi, zan danƙa ki a hannun waɗanda kike ƙinsu, waɗanda kika ƙi su, kika kuwa rabu da su.


domin haka zan bashe ku abin mallaka ga mutanen gabas. Za su kafa alfarwansu a cikinku, su zauna tare da ku. Za su ci amfanin gonakinku, su sha madararku.


domin haka zan miƙa hannuna gāba da ku, zan bashe ku, ku lalace a ƙasashe, zan hallaka ku. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”


Zan zama kamar zaki ga Ifraimu, Kamar sagarin zaki ga mutanen Yahuza. Ni kaina zan yayyage, in yi tafiyata. Zan ɗauka, in tafi, ba wanda zai yi ceto.”


Domin haka Ubangiji ya ce, Ga shi, yana shirya wa wannan jama'a masifa, Wadda ba za ku iya kuɓuta daga cikinta ba. Ba kuma za ku yi tafiyar alfarma ba, Gama mugun lokaci ne.


domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan