Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:12 - Littafi Mai Tsarki

12 “Dukanku masu wucewa, ba wani abu ba ne a gare ku? Ku duba, ku gani, ko akwai baƙin ciki irin nawa, Wanda Ubangiji ya ɗora mini, A ranar fushinsa mai zafi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 “Ko wannan ba wani abu ba ne a wurinku, dukanku masu wucewa? Ku duba ku gani. Ko akwai wata wahala kamar irin wadda nake sha, wadda Ubangiji ya auko mini a cikin zafin fushinsa?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:12
18 Iomraidhean Croise  

Hasalarka ta bi ta kaina, Tasar mini da kake ta yi, ta hallaka ni.


Zan sa sammai su yi rawar jiki, duniya kuwa za a girgiza ta a inda take, a wannan rana sa'ad da ni, Ubangiji Mai Runduna, na nuna fushina.


Tawa ta ƙare, saboda raunin da aka yi mini. Raunina mai tsanani ne, Amma na ce, lalle wannan azaba ce, Tilas in daure da ita.


Sun mai da ƙasarsu abar banƙyama, Abin raini har abada. Duk wanda ya wuce ta wurin zai razana ya kaɗa kansa.


Ga hadirin hasalar Ubangiji ya taso, wato iskar guguwa, Zai huce a kan mugaye.


Zafin fushin Ubangiji ba zai huce ba, Sai ya aikata, ya kammala abubuwan da ya yi niyya a tunaninsa. A nan gaba mutanensa za su fahimci wannan.


Kaito, gama wannan babbar rana ce, Ba kuma kamarta, Lokaci ne na wahala ga Yakubu, Duk da haka za a cece shi daga cikinta.”


Domin haka sai ku sa tufafin makoki, Ku yi makoki ku yi kuka, Gama fushin Ubangiji bai rabu da mu ba.”


Kin yi wa mutanen Isra'ila dariya. A kowane lokacin da kika ambaci sunansu, sai ki taɗa kanki da raini kamar an kama su tare da ɓarayi.


“Abin da Ubangiji ya yi daidai ne, Gama ni na ƙi bin maganarsa, Ku ji, ya ku jama'a duka, Ku dubi wahalata, 'Yan matana da samarina, An kai su bauta!


Ubangiji ya duhunta Sihiyona saboda fushinsa! Daga Sama kuma ya jefar da darajar Isra'ila a ƙasa. Bai kuma tuna da matashin sawayensa ba A ranar fushinsa.


Me zan ce miki? Da me zan kwatanta ki, ya Urushalima? Da me zan misalta wahalarki Don in ta'azantar da ke, ya Sihiyona? Masifar da ta same ki tana da fāɗi kamar teku, Wa zai iya warkar da ke?


Ya tabbatar da maganarsa wadda ya yi a kanmu da shugabanninmu waɗanda suka yi mulkinmu. Ya aukar mana da babban bala'i, gama a duniya duka ba a taɓa yin irin abin da aka yi wa Urushalima ba.


Za ta zama rana ce mai duhu dulum, Ranar gizagizai ce baƙi ƙirin. Runduna mai ƙarfi tana tasowa, Kamar ketowar hasken safiya bisa tsaunuka. Faufau ba a taɓa ganin irinta ba, Ba kuwa za a sāke ganin irinta ba.


A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan