Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Dukan jama'arta suna nishi don neman abinci, Sun ba da kayansu masu daraja saboda abinci Don su rayu. “Ya Ubangiji ka duba, ka gani, Gama an raina ni.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Dukan mutanenta suna nishi da ƙyar suna neman burodi; sun sayar da dukiyarsu don su samu abinci don kada su mutu da yunwa. “Ubangiji, ka duba ka gani, gama an yashe ni.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:11
20 Iomraidhean Croise  

Aka yi yunwa mai tsanani a Samariya a lokacin da aka kewaye ta da yaƙin, har aka riƙa sayar da kan jaki a bakin shekel tamanin, an kuma sayar da rubu'in mudu na kashin kurciya a bakin shekel biyar.


“Ai, ni ba a bakin kome nake ba, Wace amsa zan ba ka? Na rufe bakina na yi gam.


Sauran al'ummar da take kewaye da mu, Suka maishe mu abin ba'a, suka yi mana dariya, Suka yi mana ba'a.


“Domin haka ga abin da ni, Ubangiji na ce, Idan ka komo sa'an nan zan kawo ka. Za ka tsaya a gabana. Idan ka hurta abin da yake gaskiya ba na ƙarya ba, Za ka zama kakakina. Za su komo gare ka, Amma kai ba za ka koma wurinsu ba.


Zan sa su ci naman 'ya'yansu mata da maza. Kowa zai ci naman maƙwabcinsa cikin damuwa a lokacin da za a kewaye su da yaƙi, zai sha wahala daga wurin abokan gābansa da waɗanda suke neman ransa.’


“Ya maigirma sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu da suka saka annabi Irmiya cikin fijiya, Zai mutu can da yunwa, gama ba sauran abinci a birnin.”


A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci.


Urushalima ta yi zunubi ƙwarai da gaske, Saboda haka ta ƙazantu, Dukan waɗanda suka girmama ta sun raina ta Domin sun ga tsiraicinta, Ita kanta ma tana nishi, ta ba da baya.


Ƙazantarta tana cikin tufafinta, Ba ta tuna da ƙarshenta ba, Domin haka faɗuwarta abar tsoro ce, Ba ta da mai yi mata ta'aziyya. “Ya Ubangiji, ka dubi wahalata, Gama maƙiyi ya ɗaukaka kansa!”


Idanuna sun dushe saboda kuka, Raina yana cikin damuwa. Zuciyata ta karai saboda halakar mutanena, Gama 'yan yara da masu shan mama Sun suma a titunan birnin.


Suna yi wa uwayensu kuka, suna cewa, “Ina abinci da ruwan inabi?” Suna suma kamar mutanen da aka yi wa rauni A titunan birnin, Suna mutuwa a ƙirjin uwayensu.


Ya Ubangiji, ka duba, ka gani! Wane ne ka yi wa haka? Mata za su cinye 'ya'yansu da suke reno? Ko kuwa za a kashe firist da annabi A cikin Haikalin Ubangiji?


Ya Ubangiji, ka tuna da abin da ya same mu. Ka duba, ka ga yadda muka zama abin kunya!


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan