Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Maƙiyi ya miƙa hannunsa A kan dukan kayanta masu daraja, Gama ta ga al'ummai sun shiga Haikali, Su waɗanda ka hana su shiga cikin jama'arka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Maƙiya ya kwashe dukiyarta duka; ta ga mutanen da ba su san Allah ba sun shiga wuri mai tsarkinta waɗanda ka hana su shiga taron jama’arka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:10
22 Iomraidhean Croise  

Ya kwaso dukan kayayyakin da suke a Haikalin Allah, manya da ƙanana, da dukiyar da take a Haikalin Allah, da ta sarki, da ta sarakunansa ya kai su Babila.


A wannan rana aka karanta daga littafin Musa a kunnuwan jama'a. A cikinsa aka tarar da inda aka rubuta, cewa kada Ba'ammone, ko mutumin Mowab ya shiga taron jama'ar Allah.


Abokan gabanmu sun kusa su kori mutanenka gaba ɗaya sun kuma tattake Haikalinka.


Ubangiji ya ce mini, “Zan ba da wadatarku da dukiyarku ganima kyauta, saboda dukan zunubanku a dukan ƙasar.


Banda haka kuma zan ba da dukan dukiyar wannan birni, da dukan ribarsa, da dukan abubuwa masu tamani, da dukan dukiyar sarakunan Yahuza, ga abokan gābansu, waɗanda za su washe su, su kama su, su kai Babila.


Gama Ubangiji Mai Runduna ya faɗi zancen ginshiƙai, da babbar kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,


“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya faɗa a kan kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima,


Ku ji, sun gudu sun tsere daga ƙasar Babila, Don su faɗa cikin Sihiyona, Sakayyar Ubangiji Allahnmu domin Haikalinsa.


Mun sha kunya saboda zargin da ake yi mana, Kunya ta rufe mu, Gama baƙi sun shiga tsarkakan wurare na Haikalin Ubangiji.


Sai ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan manyan gidajen da suke Urushalima.


A kwanakin wahalarta na rashin wurin zama, Urushalima ta tuna da dukan abubuwanta masu daraja a dā. A lokacin da mutanenta suka fāɗa a hannun maƙiyi, Ba wanda ya taimake ta, Maƙiyanta sun gan ta, Sun yi mata ba'a saboda fāɗuwarta.


Gama kuna ƙazantar da Haikalina ta wurin shigar da baƙi marasa imani da marasa kaciya, sa'ad da kuke miƙa mini hadayu na kitse da jini. Kun ta da alkawarina da ayyukanku na banƙyama.


Zan kuwa juya daga gare su. Zan bar su su ƙazantar da Haikalina. Mafasa za su shiga su ƙazantar da shi.


Ya kuma ce musu, “Ku ƙazantar da Haikalin, ku cika farfajiya da kisassu, sa'an nan ku tafi!” Sai suka tafi, suka yi ta kashe mutanen da suke cikin birnin.


“Sa'ad da kuka ga an kafa mummunan aikin saɓo mai banƙyama a wurin da bai kamata ba (mai karatu fa yă fahimta), to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.


“Kada Ba'ammone ko Bamowabe ya shiga taron jama'ar Ubangiji. Har tsara ta goma ta zuriyarsu ba za su shiga taron jama'ar Ubangiji ba.


domin ba su zo sun tarye ku, su kawo muku abinci da ruwa ba sa'ad da kuke a hanyarku, lokacin da kuka fito daga Masar. Ga shi kuma, sun yi ijara da Bal'amu ɗan Beyor daga Fetor ta Mesofatamiya ya zo ya la'anta ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan