Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 1:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Urushalima wadda take cike da mutane a dā, Yanzu tana zaman kaɗaici! Tana zama kamar mace wadda mijinta ya rasu, Ita wadda dā ta zama babba a cikin sauran al'ummai! Ita wadda take a dā sarauniya a cikin larduna, Ta zama mai biyan gandu!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Yanzu birnin ya zama babu kowa a ciki, birnin da a dā yake cike da mutane! Yanzu birnin ya zama kamar gwauruwa, wadda a dā babba ce ita a cikin ƙasashe! Ita da take sarauniya a cikin larduna yanzu ta zama baiwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 1:1
38 Iomraidhean Croise  

Sulemanu ya sarauci dukan mulkoki tun daga Kogin Yufiretis a gabas, har zuwa ƙasar Filistiyawa a yamma, daga kudu kuma har zuwa iyakar Masar. Su kuwa suka yi ta kawo wa Sulemanu harajinsu, ya kuwa mallake su dukan kwanakin ransa.


Fir'auna-neko ya sa shi a kurkuku a Ribla a ƙasar Hamat, don kada ya yi mulki a Urushalima. Ya kuma sa ƙasar ta riƙa ba da gandu, wato haraji, talanti ɗari na azurfa da talanti guda na zinariya.


Yehoyakim yakan ba Fir'auna azurfa da zinariya, ya kuwa sa wa ƙasar haraji don ya sami kuɗin da Fir'auna ya umarta. Ya tilasta wa kowa ya biya azurfa da zinariya bisa ga yadda ya sa masa don ya ba Fir'auna-neko.


Ya mallaki dukan sarakuna tun daga Yufiretis, har zuwa ƙasar Filistiyawa har kuma zuwa kan iyakar Masar.


Manya manyan sarakuna sun yi sarauta a Urushalima, waɗanda suka yi mulki a kan dukan lardin Yammacin Kogi, waɗanda aka biya su haraji, da kuɗin shiga da fita na kaya, da kuɗin fito.


Akwai waɗansu kuma da suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu.


Amfanin ƙasa duk yana tafiya ga sarakunan Da ka ɗora su a kanmu saboda mun yi zunubi. Suna yi mana yadda suka ga dama, mu da dabbobinmu, Muna cikin baƙin ciki.”


A nan kabilai sukan zo, Kabilan Isra'ila, Domin su yi godiya ga Ubangiji, Kamar yadda ya umarce su.


Ya Sarkin Babila, kai da kake tauraron asubahi mai haske, ka fāɗo daga sama. A dā ka ci al'ummai da yaƙi amma yanzu an fyaɗa ka ƙasa.


Birnin duka ya ruguntsume, cike da hayaniya da tashin hankali. Mutanenku da suka mutu ba su mutu suna yaƙi ba.


Ƙofofin birnin za su yi makoki, su yi kuka. Za a kamanta birnin da matar da take zaune a ƙasa tsirara.


Sa'an nan za ki ce wa kanki, ‘Wa ya haifa mini waɗannan 'ya'ya? Na rasa 'ya'yana, ba kuwa zan iya haifar waɗansu ba. Aka kore ni, aka yi mini ɗaurin talala, Wane ne ya haifi waɗannan 'ya'ya? Aka bar ni, ni kaɗai, Daga ina waɗannan 'ya'ya suka fito?’ ”


Ubangiji ya ba ni fahimi, Ban kuwa yi masa tayarwa ba Ko in juya in rabu da shi.


Ki kakkaɓe kanki, ya Urushalima! Ki tashi daga cikin ƙura, Ki hau gadon sarautarki. Ki ɓaɓɓale sarƙoƙin da suke ɗaure da ke, Ke kamammiyar jama'ar Sihiyona!


Me ya fi wannan kyau? A ga manzo yana zuwa ta kan duwatsu, Ɗauke da albishir mai daɗi, labarin salama. Ya yi shelar nasara, ya ce wa Sihiyona, “Allahnki sarki ne!”


Kada ki ji tsoro, ba za a ƙara kunyatar da ke ba, Ba kuwa za a ƙasƙantar da ke ba. Za ki manta da rashin amincinki irin na matar ƙuruciya, Za ki manta da matsanancin kaɗaicinki, Mai kama da na gwauruwa.


Ga abin da Ubangiji ya ce, “Raira wa Yakubu waƙar farin ciki da ƙarfi, Ku ta da murya saboda shugaban al'ummai, Ku yi shela, ku yi yabo, ku ce, ‘Ya Ubangiji ka ceci jama'arka, Wato ringin mutanen Isra'ila,’


Gedaliya ɗan Ahikam, jikan shafan ya rantse musu da mutanensu, ya ce, “Kada ku ji tsoron bauta wa Kaldiyawa, ku yi zamanku a ƙasar, ku bauta wa Sarkin Babila, za ku kuwa zauna lafiya.


suka ce wa annabi Irmiya, “Muna roƙonka, ka roƙi Ubangiji Allahnka dominmu, dukanmu da muka ragu, gama mu kima muka ragu daga cikin masu yawa, kamar yadda kake ganinmu da idonka.


“Ni Ubangiji Mai Runduna Allah na Isra'ila, na ce, ku da kanku kun ga masifar da na aukar wa Urushalima, da dukan garuruwan Yahuza. Yanzu sun zama kufai, ba wanda yake zaune a cikinsu,


Saboda haka fushina ya yi zafi a kan garuruwan Yahuza da titunan Urushalima, don haka a yanzu sun lalace, suka zama kufai.


Ga yadda aka karya gudumar dukan duniya! Ga yadda Babila ta zama abar ƙyama ga sauran al'umma!


“Ni Ubangiji na ce, zan mai da Urushalima tsibin kufai, Wurin zaman diloli, Zan kuma mai da biranen Yahuza kufai, inda ba kowa.”


“Na kira masoyana, amma suka yaudare ni, Firistocina da dattawana a cikin birni sun hallaka Saboda neman abincin da za su ci su rayu.


Ubangiji ya duhunta Sihiyona saboda fushinsa! Daga Sama kuma ya jefar da darajar Isra'ila a ƙasa. Bai kuma tuna da matashin sawayensa ba A ranar fushinsa.


Dattawan Sihiyona suna zaune a ƙasa shiru, Sun yi hurwa, suna saye da tufafin makoki. 'Yan matan Urushalima kuma sun sunkuyar da kansu ƙasa.


Ƙaƙa zinariya ta zama duhu! Ƙaƙa zinariya tsantsa ta sāke! Tsarkakakkun duwatsu kuma suna zube A kowane magamin titi.


Rawani ya fāɗi daga kanmu, Tamu tu ƙare, gama mun yi zunubi!


Sa'an nan sarakunan bakin teku za su sauka daga gadajen sarautarsu, su tuɓe rigunansu, da rigunansu waɗanda aka yi wa ado. Za su zauna a ƙasa suna rawar jiki a kowane lokaci. Za su razana saboda abin da ya same ki.


“Ɗan mutum, da yake Taya ta yi magana a kan Urushalima ta ce, ‘Madalla, Urushalima ta rushe, ƙofa ta buɗu, yanzu zan wadata da yake ta zama kufai,’


Ubangiji Allah ya ce, “Wannan ita ce Urushalima. Na kafa ta a tsakiyar al'ummai da ƙasashe kewaye da ita.


Zan sa biranenku su zama kangwaye, in mai da wuraren yin sujada kufai, ba zan shaƙi ƙanshin turarenku ba.


Zan sa a kawo muku yaƙi a warwatsa ku a baƙin ƙasashe, ƙasarku za ta zama kufai, biranenku kuwa za su lalace.


Wannan shi ne birnin da yake da harka, mai zaman lafiya, Wanda yake ce wa kansa, “Ba wani sai ni.” Ga shi, ya zama kufai, Wurin zaman dabbobi! Duk wanda ya wuce ta wurin, Zai yi tsaki, ya kaɗa kai.


Yadda ta ɗaukaka kanta, ta yi almubazzaranci, Haka ku ma ku saka mata da azaba, da baƙin ciki gwargwadon haka. Tun da yake a birnin zuciyarta ta ce, ‘Ni sarauniya ce, a zaune nake, Ni ba gwauruwa ba ce, Ba ni da baƙin ciki kuma har abada!’


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan