Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 8:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ga shi, Allah ya ba da Oreb da Ziyib sarakunan Madayanawa a gare ku. To, me na yi wanda ya fi naku?” Da ya faɗi haka, sai suka huce.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Allah ya ba da Oreb da Zeyib, shugabannin Midiyawa a hannuwanku. Me na yi da ya fi naku? Da ya faɗi haka sai hankalinsu ya kwanta.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 8:3
15 Iomraidhean Croise  

A gare ka kaɗai, ya Ubangiji, A gare ka kaɗai, ba a gare mu ba, Dole a girmama ka, Sabili da madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.


Ba da takubansu suka ci ƙasar ba, Ba kuwa da ikonsu suka rinjayi ƙasar ba, Amma da ikonka ne da kuma ƙarfinka, Ta wurin tabbatar musu kana tare da su, Kana nuna musu kana ƙaunarsu.


Amsa magana da tattausan harshe takan kwantar da hasala, amma magana da kakkausan harshe takan kuta fushi.


Ya fi kyau ka zama mai haƙuri da ka zama mai ƙarfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.


Manufar da aka bayyana sosai kamar zubin zinariya take wanda aka yi a kan azurfa.


Rinjayen da aka yi cikin haƙuri yakan rushe ƙaƙƙarfar tsayayya, har ma yakan i wa masu ƙarfin gaske.


A nan kam, wannan karin maganar gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani da girbi.’


Albarkacin alherin da aka yi mini ina yi wa kowannenku gargaɗi kada ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, sai dai ya san kansa, gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi.


Da yake muna da baiwa iri iri, gwargwadon alherin da aka yi mana, to, sai mu yi amfani da su. In ta annabci ce, sai mu yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarmu,


Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali'u, kowa yana mai da ɗan'uwansa ya fi shi.


Amma ya ce musu, “Yanzu, me na yi fiye da ku? Ai, kalar inabin Ifraimu ta fi dukan girbin Abiyezer, wato ɗan abin da kuka yi ya fi wanda kabilata ta yi nesa.


Da Gidiyon ya zo Urdun sai ya haye tare da mutum ɗari uku ɗin nan da suke tare da shi. Ko da yake sun gaji, duk da haka suka yi ta runtumar magabta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan