Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 7:9 - Littafi Mai Tsarki

9 A wannan dare sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi, ka tafi sansanin Madayanawa, gama na ba da su gare ka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 A daren nan Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Tashi ka tafi sansaninsu domin zan ba da su a hannuwanka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 7:9
23 Iomraidhean Croise  

Ba ku za ku yi wannan yaƙi ba, ku dai, ku jā dāga, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ciwo muku, ya Yahuza da Urushalima. Kada ku ji tsoro ko ku razana, gobe ku fita ku tsaya gāba da su, gama Ubangiji yana tare da ku.’ ”


Kamar wani irin mafarki mai razanarwa yake, Wanda ya hana ni jin daɗin barcina.


Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi a mafarki, ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka, domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne.


Da suka tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu ƙasar Masar, ka zauna a can sai na faɗa maka, don Hirudus yana shirin binciko ɗan yaron yă hallaka shi.”


Don a daren jiya wani mala'ikan Allah wanda ni nasa ne, nake kuma bauta masa, ya tsaya kusa da ni,


Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu gama na riga na ba da su a hannunka, ba mutuminsu da zai iya tsayawa a gabanka.”


Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, gama gobe war haka zan ba da su ga Isra'ilawa, su karkashe su duka. Za ku daddatse agaran dawakansu, ku kuma ƙone karusansu.”


Suka kuma ce masa, “Hakika, Ubangiji ya ba da ƙasar duka a hannunmu, banda wannan kuma mazaunan ƙasar duka sun firgita saboda mu.”


Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa domin ya hukunta Isra'ilawa. Ya fita ya yi yaƙi da Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Ubangiji kuwa ya ba da sarkin a hannun Otniyel, ya rinjaye shi.


Sai ya ce musu, “Ku biyo ni, gama Ubangiji ya ba da Mowabawa maƙiyanku a gare ku.” Suka gangara, suna biye da shi. Suka ƙwace wa Mowabawa mashigan Urdun, suka hana kowa wucewa.


Amma idan kana jin tsoro ka tafi kai kaɗai, ka tafi tare da Fura, baranka.


Mutane suka ɗauki guzuri da ƙahoni, Gidiyon kuwa ya sallami sauran mutane, amma ya bar mutum ɗari uku ɗin nan. Sansanin Madayanawa kuwa yana ƙasa da su a kwarin.


Sa'an nan Jonatan ya ce, “Za mu haye zuwa wurin mutanen, mu nuna kanmu gare su.


Dawuda kuma ya sāke roƙon Ubangiji. Sai Ubangiji ya amsa masa, ya ce, “Tashi, ka gangara zuwa Kaila, gama zan ba da Filistiyawa a hannunka.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan