Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 7:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Mutane suka ɗauki guzuri da ƙahoni, Gidiyon kuwa ya sallami sauran mutane, amma ya bar mutum ɗari uku ɗin nan. Sansanin Madayanawa kuwa yana ƙasa da su a kwarin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Saboda haka Gideyon ya mai da sauran Isra’ilawa zuwa tentinsu amma ya riƙe mutum ɗari uku waɗanda suka karɓi guzuri da ƙahonin sauran. To, sansanin Midiyawa yana ƙasa da su a kwarin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 7:8
11 Iomraidhean Croise  

A wannan rana za a busa ƙaho don a kirawo Isra'ilawan da suke zaman baƙunci a Assuriya da Masar. Za su zo su yi wa Ubangiji sujada a Urushalima a tsattsarkan dutsensa.


ya ce wa Isra'ilawa su mai da rana ta fari ga wata na bakwai ta zama ranar hutu musamman, sa'ad da za su ji busar ƙaho, sai su taru domin yin sujada.


A ranar kafara, goma ga wata na bakwai za su busa ƙahon rago da ƙarfi cikin ƙasarsu duka.


Sa'ad da kuka tafi yaƙi a ƙasarku gāba da maƙiyanku da suke matsa muku lamba, sai ku yi busar faɗakarwan nan da kakakin, Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, ya cece ku daga maƙiyanku.


farat ɗaya da ƙyiftawar ido, da jin busar ƙaho na ƙarshe, domin za a busa ƙaho, za a kuma ta da matattu da halin rashin ruɓa, za a kuma sauya kamanninmu.


Jama'a suka yi ihu, aka busa ƙahoni. Nan da nan da jama'ar suka ji muryar ƙaho, suka yi ihu da babbar murya, sai garun ya rushe tun daga tushenta. Jama'a kuwa suka shiga birnin, kowanne ya nufi inda ya fuskanta sosai, suka ci birnin.


Sai firistoci bakwai su riƙe ƙahonin raguna a gaban akwatin alkawari. Amma a rana ta bakwai za ku zaga birnin sau bakwai, firistoci su yi ta busar ƙahoni.


Da ya isa can sai ya busa ƙaho a ƙasar tudu ta Ifraimu. Jama'ar Isra'ila kuwa suka gangara tare da shi daga ƙasar tudu. Yana kan gaba.


Dukan Madayanawa kuwa, da Amalekawa, da mutanen gabas suka tattaru. Suka haye, suke kafa sansaninsu a kwarin Yezreyel.


Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Gidiyon, “Da mutum ɗari uku ɗin nan da suka tanɗi ruwa zan cece ku. Zan ba da Madayanawa a gare ku, ka sallami sauran, kowa ya koma gidansa.”


A wannan dare sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi, ka tafi sansanin Madayanawa, gama na ba da su gare ka.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan