Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 7:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Sai ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho, da tulu, da jiniya a cikin tulun.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho da tulu da acibalbal a ciki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 7:16
6 Iomraidhean Croise  

Da dad dare sai ya kasa jarumawansa yadda za su gabza da su, shi da barorinsa, ya kuma ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewacin Dimashƙu.


Ya aiki runduna zuwa yaƙi. Ya sa Yowab ya shugabanci sulusi ɗaya na rundunar, sulusi na biyu kuma ya sa a hannun Abishai, ɗan Zeruya, ɗan'uwan Yowab. Sulusi na uku kuwa ya sa a hannun Ittayi Bagitte. Sa'an nan sarki ya ce wa sojojin, “Ni ma da kaina zan tafi tare da ku.”


Wannan wadata da muke da ita kuwa, a cikin kasake take, wato, jikunanmu, don a nuna mafificin ikon nan na Allah ne, ba namu ba.


Da Gidiyon ya ji mafarkin, har da fassarar, sai ya yi sujada, ya koma a sansaninsu na Isra'ilawa. Da ya isa, sai ya ce, “Ku tashi, gama Ubangiji ya ba da rundunar Madayanawa a gare ku.”


Sa'an nan ya ce musu, “Sa'ad da muka kai sansani, sai ku dube ni, ku yi duk abin da nake yi. Yadda na yi, ku ma ku yi haka.


Gari na wayewa, sai Saul ya raba mutanen kashi uku, suka fāɗa wa sansanin Ammonawa da kisa tun da sassafe har rana tsaka, aka warwatsa waɗanda suka tsira ɗaya ɗaya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan