Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 7:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Madayanawa, da Amalekawa, da mutanen gabas duka suna nan da yawa a shimfiɗe cikin kwarin, kamar fara. Raƙumansu kuma suna da yawa kamar yashi a bakin teku. Ba wanda zai iya ƙidaya su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Midiyawa, Amalekawa da dukan sauran mutane gabashi suka yi sansani a kwari, kamar fāra. Raƙumansu kuma kamar yashi a bakin teku don sun wuce ƙirge.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 7:12
16 Iomraidhean Croise  

Aka tara mutanen Isra'ila, aka ba su guzuri, suka tafi, su yi yaƙi da Suriyawa. Isra'ilawa suka kafa sansani a gabansu kamar 'yan garkuna biyu na awaki, amma Suriyawa suka cika ƙasar.


Hikimar Sulemanu ta fi ta dukan mutanen gabas, ko masu hikima na Masar.


Ina da maƙiya da yawa, ya Ubangiji, Da yawa kuma sun juya, suna gāba da ni!


Ba saboda ƙarfin mayaƙa sarki yakan ci nasara ba, Mayaƙi ba yakan yi rinjaye saboda ƙarfinsa ba.


Ni Ubangiji na ce, za su sari kurminta, Ko da yake ba su ƙirguwa, Gama suna da yawa kamar fara, Ba su lasaftuwa.


Sai suka fita tare da dukan mayaƙansu, babbar runduna mai yawa kamar yashi a bakin teku, da dawakai, da karusai da yawa ƙwarai.


Duk lokacin da Isra'ilawa suka yi shuka, sai Madayanawa, da Amalekawa, da waɗansu kabilai na hamada su zo su fāɗa musu.


Dukan Madayanawa kuwa, da Amalekawa, da mutanen gabas suka tattaru. Suka haye, suke kafa sansaninsu a kwarin Yezreyel.


Gama sukan zo da dabbobinsu da alfarwansu da yawa, kamar fara. Su da raƙumansu ba su ƙidayuwa, sukan zo, su lalatar da ƙasar.


Sa'ad da Gidiyon ya tafi, sai ya ji wani yana faɗa wa abokinsa mafarkin da ya yi. Ya ce, “Na yi mafarki, na ga wainar sha'ir ta faɗo a tsakiyar sansaninmu. Ta zo ta bugi alfarwa. Alfarwar kuwa ta fāɗi rigingine.”


Zeba da Zalmunna kuwa suna Karkor tare da rundunarsu, mutum wajen dubu goma sha biyar (15,000), waɗanda suka ragu daga cikin rundunar mutanen gabas, gama an kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000), masu takuba.


Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra'ilawa. Suka fito da karusa dubu talatin (30,000), da mahayan dawakai dubu shida (6,000), da sojoji da yawa kamar yashi a bakin teku, suka kafa sansani a Mikmash, a wajen gabashin Bet-awen.


Sai Dawuda ya yi ta karkashe su tun faɗuwar rana har zuwa kashegari da yamma. Ba wanda ya tsira daga cikinsu sai samari ɗari huɗu waɗanda suka tsere a kan raƙuma.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan