Za ka ji abin da suke cewa. Bayan haka za ka sami ƙarfin hali da za ka tafi ka fāda wa sansaninsu.” Gidiyon kuwa ya tafi tare da Fura baransa a gefen sansanin abokan gāba.
Dawuda ya ce wa Ahimelek Bahitte, da Abishai, ɗan Zeruya, ɗan'uwan Yowab, “Wa zai tafi tare da ni zuwa sansanin Saul?” Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”