Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 7:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sai Yerubba'al, wato Gidiyon, da mutanen da suke tare da shi suka yi sammako, suka kafa sansaninsu kusa da maɓuɓɓugan Harod. Madayanawa kuwa suka kafa sansaninsu a arewa da su, kusa da tudun More a kwarin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Kashegari da sassafe, Yerub-Ba’al (wato, Gideyon) da dukan mutanensa suka kafa sansani a maɓulɓulan Harod. Sansanin Midiyawa kuma yana arewa da su a kwari kusa da tudu na More.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 7:1
14 Iomraidhean Croise  

Abram ya ratsa ƙasar zuwa Shekem, wurin itacen oak na More. A lokacin nan Kan'aniyawa suke a ƙasar.


Sai Ibrahim ya tashi tun da sassafe, ya ɗaura wa jakinsa shimfiɗa ya kuwa ɗauki biyu daga cikin samarinsa tare da shi, da kuma ɗansa Ishaku, ya faskara itace na yin hadayar ƙonawa. Ya kuwa tashi ya tafi inda Allah ya faɗa masa.


Ka yi musu yadda ka yi wa Madayanawa, Ka yi musu yadda ka yi wa Sisera Da Yabin a Kogin Kishon,


Duk abin da kake iya yi, ka yi shi da iyakar iyawarka, domin ba aiki, ko tunani, ko ilimi, ko hikima a lahira, gama can za ka.


Duka biyunsu suna hayin Urdun ne, yamma da hanya a ƙasar Kan'aniyawa, mazaunan Araba, kusa da Gilgal, wajen itacen oak na More.


Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, da shi da dukan jama'ar Isra'ila, suka kama hanya daga Shittim zuwa Urdun, inda suka sauka kafin su haye.


Sai Joshuwa ya tashi da sassafe, firistocin suka ɗauki akwatin Ubangiji.


A ranar nan aka laƙaba wa Gidiyon suna Yerubba'al, wato “Bari gunki Ba'al ya yi hamayya don kansa, domin an farfashe bagadensa.”


Dukan Madayanawa kuwa, da Amalekawa, da mutanen gabas suka tattaru. Suka haye, suke kafa sansaninsu a kwarin Yezreyel.


Haka kuwa Allah ya yi a daren. Aka yi raɓa a ƙasa, amma ulun yana a bushe.


Gidiyon kuwa ya tafi ya zauna a gidansa na kansa.


Ubangiji kuwa ya aika musu da Yerubba'al, wato Gidiyon, da Barak, da Yefta, da Samson, suka cece ku daga hannun abokan gābanku ta kowace fuska. Sa'an nan kuka yi zamanku lafiya.


Filistiyawa suka tattara rundunar yaƙinsu a Afek. Isra'ilawa kuma suka kafa sansaninsu kusa da maɓuɓɓugar da take a Yezreyel.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan