Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 5:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Isra'ilawa suka ƙudura su yi yaƙi. Mutane suka sa kansu da farin ciki. Alhamdu lillahi!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 “Sa’ad da ’ya’yan sarki a Isra’ila suka yi jagora, sa’ad da mutane suka niyya su ba da kansu, suna yabon Ubangiji!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 5:2
23 Iomraidhean Croise  

Mai biye da Yehohanan kuma shi ne shugaba Amasiya, ɗan Zikri, wanda ya ba da kansa don bauta wa Ubangiji, shi kuma yana shugabancin sojoji dubu ɗari biyu (200,000) gwarzaye.


Jama'a suka sa wa dukan waɗanda suka tafi su zauna a Urushalima da yardar ransu albarka.


Ka yabi Ubangiji, ya raina, Kada ka manta da yawan alherinsa.


A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka, Jama'arka za su kawo maka gudunmawa don kansu. Kamar yadda raɓa take da sassafe, Haka samarinka za su zo wurinka a tsarkakan tsaunuka.


Shi ne ya sa ruwa ya ci Fir'auna da rundunarsa, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.


Yakan ba ni nasara a kan magabtana, Yakan sa jama'a a ƙarƙashina,


Bari jama'ar Sihiyona su yi murna! Gama kana shari'a ta gaskiya, Bari biranen Yahuza su yi farin ciki.


Ya Ubangiji, kai Allah ne wanda yake yin hukunci, Ka bayyana fushinka!


Jama'ar Sihiyona suna murna, Garuruwan Yahuza kuma suna farin ciki, Sabili da irin shari'unka, ya Ubangiji!


Da da ra'ina nake yi, da sai a biya ni. Amma da yake ba da ra'ina ba ne, an danƙa mini amana ke nan.


Domin mutum yana da niyyar bayarwa, bayarwarsa za ta zama abar karɓa ce, bisa ga yawan abin da yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.


Sai kowa yă bayar yadda ya yi niyya, ba tare da ɓacin rai ko tilastawa ba, domin Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.


“Ya ku al'ummai, ku yabi jama'arsa, Gama zai rama wa bayinsa saboda jininsu, Zai ɗauki fansa a kan magabtansa, Zai tsarkake ƙasar jama'arsa.”


Zai zaɓar wa kansa wuri mai kyau, Gama wurin ne aka keɓe wa shugaba. Ya zo wurin shugabannin mutane, Tare da Isra'ila, ya aikata adalcin Ubangiji, Ya kiyaye farillansa.”


Domin Allah shi ne mai aiki a zukatanku, ku nufi abin da yake kyakkyawan nufinsa, ku kuma aikata shi.


Amma ba na so in yi kome ba tare da yardarka ba, don kada alherinka yă zamana na tilas ne, ba na ganin dama ba.


Ki yi farin ciki saboda an yi masa haka, ya sama! Ku yi farin ciki, ku tsarkaka da manzanni da annabawa, domin Allah ya rama muku abin da ya yi muku!”


Don hukuncinsa daidai yake, na adalci ne, Ya hukunta babbar karuwar nan wadda ta ɓata duniya da fasikancinta, Ya kuma ɗauki fansar jinin bayinsa a kanta.”


Zuciyata tana wajen shugabannin yaƙi na Isra'ila, Da mutanen da suka ba da kansu da farin ciki. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan