Sai Hilkiya firist, da Ahikam, da Akbor, da Shafan, da Asaya suka tafi wurin annabiya Hulda, matar Shallum ɗan Tikwa, wato jikan Harhas, mai tsaron ɗakin da ake ajiye tufafi. A Urushalima take zaune a sabuwar unguwa. Suka kuwa yi magana da ita.
“Ya Allahna, ka tuna da Tobiya da Sanballat bisa ga abubuwan nan da suka yi, da annabiya Nowadiya, da sauran annabawa waɗanda suka so su tsoratar da ni.”
Akwai kuma wata annabiya, mai suna Hannatu, 'yar Fanuyila, na kabilar Ashiru. Ta kuwa tsufa ƙwarai, ta yi zaman aure shekara bakwai bayan ɗaukanta na budurci,
Sa'an nan jama'ar Isra'ila suka yi kuka ga Ubangiji suna neman taimako, gama Yabin yana da karusai ɗari tara na ƙarfe, ya kuma tsananta wa Isra'ilawa, ya mugunta musu shekara ashirin. Isra'ilawa kuwa suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.