Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 4:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sa'an nan jama'ar Isra'ila suka yi kuka ga Ubangiji suna neman taimako, gama Yabin yana da karusai ɗari tara na ƙarfe, ya kuma tsananta wa Isra'ilawa, ya mugunta musu shekara ashirin. Isra'ilawa kuwa suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Domin Yabin sarkin Kan’ana yana da kekunan yaƙin ƙarfe ɗari tara, ya ji wa Isra’ilawa ƙwarai har shekara ashirin, sai suka yi kuka ga Ubangiji, don taimako.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 4:3
19 Iomraidhean Croise  

Abokan gābansu suka zalunce su, Suka tilasta su, su yi musu biyayya.


Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo, Zan cece ku, Ku kuwa za ku yabe ni.”


Amma sa'ad da ya kashe waɗansunsu, Sai sauran suka juyo gare shi suka tuba, Suka yi addu'a sosai a gare shi.


Ana nan, a kwana a tashi, sai Sarkin Masar ya rasu. Jama'ar Isra'ila suka yi nishi, suka yi kuka kuma saboda bautarsu, kukansu na neman gudunmawa ya kai gun Allah.


Da tsakar rana za ku riƙa lalubawa kamar makaho, ba za ku yi arziki cikin ayyukanku ba. Za a riƙa zaluntarku, ana yi muku ƙwace kullum, ba wanda zai cece ku.


Mutanen da ba ku sani ba, su za su ci amfanin gonakinku da dukan amfanin wahalarku. Za a zalunce ku, a murƙushe ku kullum.


Sai mutanen kabilan Yusufu suka ce, “Ƙasar tuddai ba ta ishe mu ba, ga kuma Kan'aniyawa da suke zaune a filin, da waɗanda suke a Bet-sheyan da ƙauyukanta, da waɗanda suke cikin Kwarin Yezreyel suna da karusan ƙarfe.”


Ubangiji kuwa yana tare da Yahuza, ya mallaki ƙasar tuddai, amma bai iya korar waɗanda suke zaune a fili ba, domin suna da karusan ƙarfe.


Sa'an nan Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suna cewa, “Mun yi maka zunubi, gama mun bar binka, ya Allahnmu, muka yi wa Ba'al sujada.”


Sa'an nan suka zubar da gumakan da suke wurinsu, suka yi wa Ubangiji sujada. Shi kuwa ya damu saboda azabar da Isra'ilawa suke sha.


Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, ya ba su wanda zai cece su, wato Ehud, ɗan Gera daga kabilar Biliyaminu, shi kuwa bahago ne. Isra'ilawa suka aika wa Eglon Sarkin Mowab da kyautai ta hannun Ehud.


Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, sai Ubangiji ya ta da Otniyel, ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu don ya ceci Isra'ilawa.


Sai Sisera ya tattaro karusansa na ƙarfe duka guda ɗari tara, da dukan mutanen da suke tare da shi, tun daga Haroshet ta al'ummai, har zuwa Kogin Kishon.


Debora, matar Lafidot, ita ce annabiya. Tana hukuncin Isra'ilawa.


Sa'ad da Isra'ilawa suka zaɓi baƙin alloli, Sai ga yaƙi a ƙasar. Ba a ga garkuwa ko mashi A wurin mutum dubu arba'in na Isra'ila ba.


Isra'ilawa suka sha ƙasƙanci ƙwarai a hannun Madayanawa. Sai suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.


suka ce wa Sama'ila, “Ka yi ta roƙo ga Ubangiji Allahnmu don ya cece mu daga hannun Filistiyawa.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan