Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 4:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Ubangiji kuwa ya yarda Yabin Sarkin Kan'ana, wanda yake mulkin Hazor ya ci su da yaƙi. Sisera, wanda yake zaune a Haroshet ta al'ummai, shi ne shugaban sojojin Yabin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Saboda haka Ubangiji ya sayar da su ga Yabin sarkin Kan’ana wanda yake mulki a Hazor. Shugaban mayaƙansa shi ne Sisera, wanda yake zaune a Haroshet Haggoyim.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 4:2
11 Iomraidhean Croise  

Ka yi musu yadda ka yi wa Madayanawa, Ka yi musu yadda ka yi wa Sisera Da Yabin a Kogin Kishon,


Ubangiji ya ce, “Kuna tsammani na kori mutanena Kamar yadda mutum yakan saki mata tasa? To, in haka ne ina takardar kisan auren? Kuna tsammani na sayar da ku cikin bauta Kamar mutumin da ya sayar da 'ya'yansa? A'a, kun tafi bauta ne saboda da zunubanku, Aka tafi da ku saboda da laifofinku.


Da yake ya gagara biya, sai ubangidansa ya yi umarni a sayar da shi da mata tasa da 'ya'yansa da kuma duk abin da ya mallaka, a biya kuɗin.


Sa'ad da Yabin Sarkin Hazor ya ji labari, ya aika wa Yobab, Sarkin Madon, da Sarkin Shimron, da Sarkin Akshaf,


da Adama, da Rama, da Hazor,


Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya ba da su ga Filistiyawa, da Ammonawa.


Sai Sisera ya tattaro karusansa na ƙarfe duka guda ɗari tara, da dukan mutanen da suke tare da shi, tun daga Haroshet ta al'ummai, har zuwa Kogin Kishon.


Amma Barak ya runtumi karusan da rundunar har zuwa Haroshet ta al'ummai. Aka kashe dukan rundunar Sisera da takobi, ba wanda ya tsira.


Amma suka bar bin Ubangiji Allahnsu. Ubangiji kuwa ya bashe su a hannun Sisera, shugaban rundunar Yabin, Sarkin Hazor, da a hannun Filistiyawa, da kuma a hannun Sarkin Mowab, suka yāƙe su.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan