Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 3:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, sai Ubangiji ya ta da Otniyel, ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu don ya ceci Isra'ilawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Amma da suka yi kuka ga Ubangiji, sai ya tad musu da mai ceto, Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kaleb wanda ya cece su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 3:9
15 Iomraidhean Croise  

Saboda haka ka bar abokan gābansu su ci su, mallake su. A wahalarsu sun yi kira gare ka domin taimako, Ka kuwa amsa musu daga Sama. Ta wurin jinƙanka mai yawa ka aiko musu da shugabanni, Waɗanda suka kuɓutar da su daga maƙiyansu.


Suka yi kira gare ka, suka tsira daga hatsari, Suka dogara gare ka, ba su kuwa kunyata ba.


Amma sa'ad da ya kashe waɗansunsu, Sai sauran suka juyo gare shi suka tuba, Suka yi addu'a sosai a gare shi.


Otniyel kuwa, ɗan Kenaz, ɗan'uwan Kalibu, ya ci Kiriyat-sefer. Kalibu kuwa ya ba shi Aksa 'yarsa aure.


Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu ya ci birnin da yaƙi, Kalibu kuwa ya ba shi 'yarsa Aksa aure.


Sa'an nan Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suna cewa, “Mun yi maka zunubi, gama mun bar binka, ya Allahnmu, muka yi wa Ba'al sujada.”


Sa'an nan Ubangiji ya naɗa musu mahukunta masu ƙarfi da suka cece su daga waɗanda suka washe su.


Sa'ad da Ubangiji ya naɗa musu mahukunci, yakan taimake shi, ya kuwa cece su daga abokan gāba dukan kwanakin mahukuncin. Gama Ubangiji ya ji ƙansu saboda nishinsu, da zaluncin da ake yi musu.


Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, ya ba su wanda zai cece su, wato Ehud, ɗan Gera daga kabilar Biliyaminu, shi kuwa bahago ne. Isra'ilawa suka aika wa Eglon Sarkin Mowab da kyautai ta hannun Ehud.


Domin haka Ubangiji ya husata ƙwarai da Isra'ilawa, sai ya bashe su ga Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Jama'ar Isra'ila kuwa suka bauta masa shekara takwas.


Sa'an nan jama'ar Isra'ila suka yi kuka ga Ubangiji suna neman taimako, gama Yabin yana da karusai ɗari tara na ƙarfe, ya kuma tsananta wa Isra'ilawa, ya mugunta musu shekara ashirin. Isra'ilawa kuwa suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.


Da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji saboda wahalar da Madayanawa suke ba su,


Sai suka yi wa Ubangiji kuka, suka ce, ‘Mun yi laifi domin mun bar bin Ubangiji, muka bauta wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot, amma yanzu muna roƙonka ka cece mu daga hannun abokan gābanmu, mu kuwa za mu bauta maka.’


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan