Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 3:4 - Littafi Mai Tsarki

4 don a jarraba Isra'ilawa da su, a gani ko za su yi biyayya da umarnan Ubangiji da ya ba kakanninsu ta hannun Musa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 An bar su domin su gwada Isra’ilawa a ga ko za su yi biyayya da umarnin Ubangiji, wanda ya ba wa kakanninsu ta wurin Musa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 3:4
7 Iomraidhean Croise  

Musa ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sa'an nan Musa ya karyi itacen, ya jefa cikin ruwa, ruwan kuwa ya zama mai daɗi. A nan ne Ubangiji ya kafa musu dokoki da ka'idodi, a nan ne kuma ya gwada su.


Don lalle ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda suke amintattu a cikinku.


A kan Lawi ya ce, “Ka ba Mai Tsarki Tumminka da Urim naka, Shi wanda ka jarraba a Masaha, Wanda ka yi jayayya da shi a ruwan Meriba,


Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.


Da haka ne zan jarraba Isra'ilawa, in gani ko za su mai da hankali su yi tafiya cikin hanyata, kamar yadda kakanninsu suka yi, ko kuwa ba za su yi ba.”


Ubangiji ya bar waɗansu al'ummai a ƙasar domin ya jarraba Isra'ilawan da ba su san yaƙin Kan'ana ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan