Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 3:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Al'umman da suka ragu a ƙasar su ne, birane biyar na Filistiyawa, da dukan Kan'aniyawa, da Sidoniyawa, da Hiwiyawa da suke zaune a Dutsen Lebanon, tun daga Dutsen Ba'alharmon har zuwa mashigin Hamat,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 sarakuna biyar na Filistiyawa, dukan Kan’aniyawa, Sidoniyawa, da kuma Hiwiyawan da suke zaune a duwatsun Lebanon daga Dutsen Ba’al-Hermon zuwa Lebo Hamat.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 3:3
31 Iomraidhean Croise  

“Zabaluna zai zauna a gefen teku, Zai zama tashar jiragen ruwa, Kan iyakarsa kuma zai kai har Sidon.


Suka tafi kagarar Taya da dukan garuruwan Hiwiyawa, da na Ƙan'aniyawa. Daga can suka tafi ƙasar kudu ta Yahuza a Biyer-sheba.


Sa'an nan kuma Sulemanu ya yi biki na kwana bakwai, shi da dukan jama'ar Isra'ila. Mutane suka zo, tun daga Mashigin Hamat a arewa, har zuwa iyakar ƙasar Masar a kudu, suka hallara a gaban Ubangiji Allahnmu.


Dukan Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, da suka ragu a ƙasar, wato waɗanda ba mutanen Isra'ila ba, waɗanda mutanen Isra'ila ba su iya hallakarwa ba, Sulemanu ya sa zuriyarsu su yi aikin tilas na bauta, haka kuwa suke har wa yau.


“A wajen yamma, Bahar Rum shi ne iyakar zuwa ƙofar Hamat. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.


Amalekawa suna zaune a Negeb, Hittiyawa kuwa, da Yebusiyawa, da Amoriyawa suna zaune a ƙasar tuddai, Kan'aniyawa suna zaune kusa da teku, da kuma kusa da Kogin Urdun.”


Daga Dutsen Hor iyakar za ta bi zuwa Hamat ta tsaya a Zedad.


Ku tashi, ku yi gaba zuwa ƙasar duwatsun Amoriyawa, da dukan maƙwabtansu waɗanda suke a Araba. Ku shiga tuddai, da kwaruruka, da Negeb, da bakin bahar, da ƙasar Kan'aniyawa, da Lebanon, har zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis.


(Sidoniyawa suka kira Harmon, Siriyon, amma Amoriyawa suna ce da shi Senir.)


Ba wani birnin da ya yi amana da Isra'ilawa, sai dai Hiwiyawa da suke zaune a Gibeyon. Saura duka kuwa, an ci su da yaƙi.


Ya kuma aika zuwa ga Kan'aniyawan da suke gabas da yamma, da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa da suke ƙasar tuddai, da Hiwiyawa da suke zaune a gindin Dutsen Harmon a ƙasar Mizfa.


daga Shihor da yake gabas da Masar zuwa iyakar Ekron a wajen arewa. Wannan ƙasa ta Kan'aniyawa ce. Akwai ƙasar sarakuna biyar na Filistiyawa da yake a Gaza, da Ashdod, da Ashkelon, da Gat, da Ekron, da ƙasar Awwiyawa,


da ƙasar Gebaliyawa, da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba'al-gad a gindin Dutsen Harmon zuwa iyakar Hamat,


da Hebron, da Rehob, da Hammon, da Kana, har ta bi ta Sidon Babba.


Amma Isra'ilawa suka ce wa Hiwiyawa, “Watakila kuna zaune a tsakiyarmu ne, to, ƙaƙa za mu yi muku alkawari?”


da Sidoniyawa, da Amalekawa, da Mawonawa ba, wato su da suka matsa muku a dā, ku kuma kuka yi kuka gare ni?


Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya ba da su ga Filistiyawa, da Ammonawa.


Iyayensa ba su san al'amarin nan daga wurin Ubangiji ne ba, gama Ubangiji yana so wannan ya zama sanadin yaƙi da Filistiyawa, gama a lokacin nan Filistiyawa ne suke mulkin Isra'ilawa.


Saboda haka mutanen nan biyar suka tashi, suka zo Layish, suka ga mutane suna zamansu a huce, kamar Sidoniyawa. Ba su da rigima, natsattsu ne, ba su jayayya da kowa, suna da wadata. Suna nesa da Sidoniyawa, ba su sha'anin kome da kowa.


Ya yi haka ne domin ya koya wa tsararrakin Isra'ila yaƙi, wato waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba.


Ubangiji kuwa ya yarda Yabin Sarkin Kan'ana, wanda yake mulkin Hazor ya ci su da yaƙi. Sisera, wanda yake zaune a Haroshet ta al'ummai, shi ne shugaban sojojin Yabin.


Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra'ilawa. Suka fito da karusa dubu talatin (30,000), da mahayan dawakai dubu shida (6,000), da sojoji da yawa kamar yashi a bakin teku, suka kafa sansani a Mikmash, a wajen gabashin Bet-awen.


Sa'ad da sarakunan Filistiyawa suke wucewa da rundunarsu na mutum ɗari ɗari da na mutum dubu dubu, Dawuda kuma da mutanensa suna biye a baya tare da Akish.


Sarakunan nan biyar na Filistiyawa sun ga an yi wannan, sa'an nan suka koma Ekron a ran nan.


Suka kai siffofin ɓerayen nan na zinariya kuwa domin garuruwa biyar masu garu da ƙauyuka marasa garu na sarakunan Filistiyawa. Babban dutse inda suka ajiye akwatin Ubangiji yana nan har wa yau a saurar Joshuwa Bet-shemesh.


Suka ce, “Wace irin hadaya za mu bayar?” Firistocin suka ce, “Sai ku yi marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa, gama annoba iri ɗaya ce ta same ku da sarakunanku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan