Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 3:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Ubangiji ya bar waɗansu al'ummai a ƙasar domin ya jarraba Isra'ilawan da ba su san yaƙin Kan'ana ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Waɗannan su ne al’umman da Ubangiji ya bari don yă gwada duk waɗannan Isra’ilawan da ba su san yaƙi a Kan’ana ba

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 3:1
20 Iomraidhean Croise  

A kan 'yan saƙon sarakunan Babila kuwa, waɗanda aka aiko su don su bincika irin abin al'ajabi da ya faru a ƙasar, sai Allah ya ƙyale shi kurum don ya jarraba shi, ya san dukan abin da suke a zuciyarsa.


Duk da haka Allah ya san kowane irin hali da nake ciki. Idan ya jarraba ni zai tarar ni tsattsarka ne.


Musa ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sa'an nan Musa ya karyi itacen, ya jefa cikin ruwa, ruwan kuwa ya zama mai daɗi. A nan ne Ubangiji ya kafa musu dokoki da ka'idodi, a nan ne kuma ya gwada su.


Zinariya da azurfa da wuta ake gwada su, zuciyar ɗan adam kuwa Ubangiji ne yake gwada ta.


Ubangiji ya ce wa Irmiya, “Na maishe ka mai aunawa da mai jarraba mutanena Domin ka sani, ka auna al'amuransu,


Sulusi ɗayan da ya ragu kuwa zan tura cikin wuta, Zan tace su da wuta kamar yadda akan tace azurfa, Zan gwada su kamar yadda akan gwada zinariya. Za su kira gare ni, Zan kuwa amsa musu, Zan ce, ‘Su jama'ata ne,’ Su kuma za su ce, ‘Ubangiji shi ne Allahnmu.’ ”


Amma Yesu bai amince da su ba,


Ubangiji Allahnku zai kori waɗannan al'ummai a gabanku da kaɗan da kaɗan. Ba za ku hallaka su gaba ɗaya ba, don kada namomin jeji su yaɗu, su dame ku.


Ya ciyar da ku da manna a jeji, abin da kakanninku ba su sani ba, domin ya koya muku tawali'u, ya jarraba ku, don ya yi muku alheri daga baya.


Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.


Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne (wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta), domin bangaskiyar nan taku tă jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu.


Ya ƙaunatattuna, kada ku yi mamakin matsananciyar wahalar da ta same ku a kan gwaji, kamar wani baƙon abu ne yake faruwa a gare ku.


Zan kashe 'ya'yanta tashi ɗaya, dukan ikilisiyoyi kuma za su sani Ni ne mai fayyace birnin zuciya. Zan kuma saka wa kowannenku gwargwadon aikinsa.


Bayan da Joshuwa ya rasu, jama'ar Isra'ila suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne daga cikinmu zai fara tafiya don ya yaƙi Kan'aniyawa?”


Dukan tsarar Joshuwa sun rasu, waɗanda suke tasowa kuwa suka manta da Ubangiji da abubuwan da ya yi wa Isra'ila.


Don haka Ubangiji ya bar waɗannan al'ummai, bai kore su nan da nan ba, bai kuma ba da su ga Joshuwa ba.


Ya yi haka ne domin ya koya wa tsararrakin Isra'ila yaƙi, wato waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan