Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 2:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Don haka na ce, ‘Ba zan kore muku su ba, amma za su zamar muku ƙaya, gumakansu kuwa za su zamar muku tarko.’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Saboda haka ina gaya muku cewa ba zan kore su a gabanku ba; za su zama muku ƙaya, gumakansu kuma za su zama muku tarko.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 2:3
11 Iomraidhean Croise  

Jama'ar Allah suka yi wa gumaka sujada. Wannan kuwa ya jawo musu hallaka.


Kada su zauna cikin ƙasarku domin kada su sa ku ku yi mini zunubi, ku bauta wa allolinsu, har abin kuwa ya zamar muku tarko.”


Ku fa kula da kanku, kada ku kuskura, ku ƙulla alkawari da mazaunan ƙasar inda za ku tafi, don kada su zama muku alƙalai.


Amma idan ba ku kori mazaunan ƙasar daga gabanku ba, to, waɗannan da kuka bari cikinta za su zama haki a idanunku, da ƙayayuwa a kwiyaɓunku. Za su yi ta wahalshe ku da yaƙi.


Sai ku hallaka dukan mutanen da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku. Kada ku ji tausayinsu. Kada kuma ku bauta wa gumakansu, don kada su zamar muku tarko.


to, sai ku tabbata Ubangiji Allahnku ba zai dinga korar al'umman nan daga gabanku ba, za su zama muku azargiya, da tarko, da bulala a kwiyaɓunku, da ƙayayuwa a idanunku. Da haka za ku ƙare sarai daga cikin kyakkyawar ƙasan nan da Ubangiji Allahnku ya ba ku.


don haka daga nan gaba ba zan ƙara kore musu wata al'umma daga cikin al'umman da Joshuwa ya rage kafin rasuwarsa ba.


Da mala'ikan Ubangiji ya faɗa wa Isra'ilawa wannan magana, suka yi kuka mai zafi.


Suka yi aurayya da su, suka kuma yi sujada ga gumakansu.


Gidiyon kuwa ya yi gunki da zinariyar, ya ajiye a birninsa, wato Ofra. Isra'ilawa kuma suka bar bin Allah, suka tafi can domin su yi wa gunkin sujada, ya zama tarko ga Gidiyon da iyalinsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan