Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 2:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Mala'ikan Ubangiji ya haura daga Gilgal zuwa Bokim. Ya ce wa Isra'ilawa, “Ni na kawo ku daga Masar zuwa ƙasar da na rantse zan ba kakanninku. Na kuma ce, ‘Ba zan ta da madawwamin alkawarina da ku ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Mala’ikan Ubangiji ya haura daga Gilgal zuwa Bokim ya ce, “Na hauro da ku daga Masar zuwa ƙasar da na rantse zan ba wa kakanninku. Na ce, ‘Ba zan taɓa tā da yarjejjeniyata da ku ba,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 2:1
41 Iomraidhean Croise  

Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Sai ya gina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.


Sai ta kira sunan Ubangiji wanda ya yi magana da ita, “Kai Allah ne mai gani,” gama ta ce, “Ni! Har na iya ganin Allah in rayu?”


Mala'ikan da ya fanshe ni Daga dukan mugunta, Ya sa wa samarin albarka, Bari a dinga ambatarsu da sunana, Da sunan Ibrahim da na Ishaku iyayena, Bari kuma su riɓaɓɓanya, su zama taron jama'a a tsakiyar duniya.”


Ka ce, “Na yi alkawari da mutumin da na zaɓa, Na yi wa bawana Dawuda alkawari cewa,


Ba zan keta alkawarin da na yi masa ba, Ba zan soke ko ɗaya daga cikin alkawaran da na yi masa ba.


Ubangiji zai yi yaƙi dominku, sai dai ku tsaya kurum!”


Mala'ikan Allah kuwa wanda yake tafiya a gaban rundunar Isra'ila ya tashi ya koma bayansu, haka kuma al'amudin girgijen ya tashi daga gabansu ya tsaya a bayansu.


“Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.


“Ni da kaina zan aiki mala'ika a gabanku don ya kiyaye ku a sa'ad da kuke tafiya, ya kuma kai ku inda na shirya muku.


Ubangiji kuwa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma hutashe ka.”


daga dukan wahalar da suke sha. Ba mala'ika ne ya cece su ba, amma Ubangiji ne. Da ƙaunarsa da juyayinsa ya fanshe su. A koyaushe yake lura da su a dā,


Saboda darajar sunanka, kada ka wulakanta mu, Kada kuma ka ƙasƙantar da darajar kursiyinka, Ka tuna da alkawarin da ka yi mana, Kada ka ta da shi.


sa'an nan zan tuna da alkawarina wanda na yi wa Yakubu, da Ishaku, da Ibrahim, zan kuwa tuna da ƙasar.


Duk da haka, sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu ba zan wulakanta su ba, ba kuwa zan ji ƙyamarsu, har da zan karya alkawarina da su ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu.


Sa'an nan na ɗauki sandana, wato “Alheri,” na karya shi, alama ke nan da ta nuna na keta alkawarin da na yi wa al'ummai duka.


A kan wannan ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya amsa, ya ce, “Zan aiki manzona don ya shirya mini hanya, sa'an nan Ubangiji wanda kuke nema zai zo farat ɗaya a cikin Haikalinsa. Manzon da kuke sa zuciyar zuwansa, yana zuwa, zai yi shelar alkawarina.”


Bisa ga kwanakin nan arba'in da kuka leƙi asirin ƙasar, haka za ku ɗauki alhakin zunubanku shekara arba'in, gama kowane kwana a maimakon shekara yake. Ta haka za ku sani ban ji daɗin abin da kuka yi ba.


Duba, na sa ƙasar a gabanku, sai ku shiga ku mallake ta, ƙasa wadda na rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, cewa zan ba su, su da zuriyarsu a bayansu.’ ”


Ko kuma, da akwai wani allah wanda ya taɓa ƙoƙarin fitar da al'umma saboda kansa daga cikin tsakiyar wata al'umma ta wurin wahalai, da alamu, da mu'ujizai, da yaƙi, da nuna iko, da babbar razana kamar yadda Ubangiji Allahnku ya yi dominku a ƙasar Masar a kan idonku duka?


Domin haka sai ku sani Ubangiji Allahnku shi ne Allah, Allah mai aminci, mai cika alkawari, mai nuna ƙauna ga dubban tsararraki waɗanda suke ƙaunarsa, suna kuma kiyaye umarnansa.


Joshuwa kuma ya ƙara da cewa, “Ta haka za ku sani Allah mai rai yana tsakiyarku, ba makawa kuwa zai kori Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Hiwiyawa, da Ferizziyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Yebusiyawa a gabanku.


Kai ba za ka mallaki abin da Kemosh, allahnka, ya ba ka mallaka ba? Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya mallakar mana, za mu mallake shi.


Akwai wani mutumin Zora daga kabilar Dan, sunansa Manowa, matarsa bakarariya ce, ba ta haihuwa.


Ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare ta, ya ce mata, “Ga shi, ke bakarariya ce, ba ki haihuwa, amma yanzu za ki yi ciki, za ki kuwa haifi ɗa.


Saboda haka suka sa wa wuri suna Bokim, wato waɗanda suke kuka. Suka kuma miƙa sadakoki ga Ubangiji a wurin.


sai Ubangiji ya aika musu da wanda ya faɗa musu saƙon Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ni ne na fito da ku daga bauta a Masar.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan