Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 18:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Ya ce musu, “Mun yi yarjejeniya da Mika, in yi masa aikin firist, shi kuma ya biya ni.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Ya gaya musu abin da Mika ya faɗa masa ya ce, “Ya ɗauke ni aiki ya kuma sa in zama masa firist.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 18:4
16 Iomraidhean Croise  

Nuna sonkai mugun abu ne, waɗansu alƙalai sukan aikata mugunta saboda 'yar ƙaramar rashawa.


Suna kama da karnuka masu zarin ci, ba su taɓa samun abin da ya ishe su ba. Makiyayan nan kuma ba haziƙai ba ne, dukansu, kowa ya nufi inda ya ga dama. Kowa yana ta nemar wa kansa riba.


Kun saɓi sunana a cikin mutanena don a tafa muku sha'ir, a ba ku ɗan abinci. Kuna kashe mutane waɗanda bai kamata su mutu ba, kuna barin waɗanda bai kamata su rayu ba ta wurin ƙaryace-karyacen da kuke yi wa mutanena waɗanda suke kasa kunne ga ƙaryace-ƙaryacen.’


“Da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin Haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ban ji daɗinku ba. Ba zan karɓi hadayun da kuke kawo mini ba,” in ji Ubangiji Mai Runduna.


Ban yi ƙyashin kuɗin kowa ba, ko kuwa tufafin wani.


Ba mashayi ba, ba mai saurin dūka ba, amma salihi, ba kuma mai husuma ba, ba kuwa mai son kuɗi ba.


Lalle ne a kwaɓe su, tun da yake suna jirkitar da jama'a gida gida, ta wurin koyar da abin da bai kamata ba, don neman ƙazamar riɓa.


Mahaɗantan malaman nan na ƙarya za su ribace ku da tsararrun labarunsu. An riga an yanke hukuncinsu tun dā, wanda zai hallaka su a shirye yake sosai.


Mika ya ce masa, “Ka zauna tare da ni, ka zama mai ba ni shawara, da kuma firist, ni kuwa zan riƙa ba ka azurfa goma, da tufafi, da abin zaman gari kowace shekara.”


Mika kuma ya naɗa shi ya zama firist ɗinsa. Ya kuwa zauna a gidansa.


Sa'ad da suke a gidan Mika ɗin, sai suka ji muryar saurayin nan, Balawe, suka tsaya suka tambaye shi, “Wa ya kawo ka nan? Me kuma kake yi a nan?”


Suka ce masa, “In ka yarda ka roƙar mana Allah ko tafiyarmu na da sa'a.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan