Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 18:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Sai Danawa suka zaɓi mutum biyar jarumai daga kabilarsu, suka aike su daga Zora da Eshtawol, su tafi leƙen asirin ƙasar, su bincike ta. Suka kuwa tafi zuwa ƙasar tudu ta Ifraimu, suka sauka a gidan Mika.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Saboda haka mutanen Dan suka aika jarumawa guda biyar daga Zora da Eshtawol don su leƙi asirin ƙasar su kuma bincike ta. Waɗannan mutanen sun wakilci dukan kabilar. Suka ce musu, “Ku je, ku bincike ƙasar.” Mutanen suka shiga ƙasar tudu ta Efraim suka zo gidan Mika, inda suka kwana.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 18:2
20 Iomraidhean Croise  

Sai Yusufu ya tuna da mafarkan da ya yi a kansu, ya ce musu, “Ku magewaya ne, zuwa kuka yi domin ku leƙi asirin ƙasar.”


Ka nemi kyakkyawar shawara za ka yi nasara, kada ka jefa kanka cikin yaƙi ba tare da shiri ba.


Sa'ad da Musa ya aike su leƙen asirin ƙasar Kan'ana, ya ce musu, “Ku haura, ku bi ta Negeb har zuwa ƙasar tuddai,


“Ko kuwa wane sarki ne, in za shi yaƙi da wani sarki, da fari ba ya zauna ya yi shawara, ya ga ko shi mai mutum dubu goma zai iya karawa da mai dubu ashirin ba?


Na filayen kwarin kuwa, su ne Eshtawol, da Zora, da Ashna,


Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar gādonta ke nan, da Zora, da Eshtawol, da Ir-shemesh,


Sai Joshuwa ɗan Nun ya aiki mutum biyu 'yan leƙen asirin ƙasa daga Shittim a asirce, ya ce musu, “Tafi, ku leƙo asirin ƙasar, musamman Yariko.” Suka tafi, suka shiga gidan wata mace, karuwa, sunanta Rahab, a nan suka sauka.


Sai aka faɗa wa Sarkin Yariko, aka ce, “Ga waɗansu mutane sun shigo nan da daddare domin su bincike ƙasar.”


Akwai wani mutumin Zora daga kabilar Dan, sunansa Manowa, matarsa bakarariya ce, ba ta haihuwa.


Ruhun Ubangiji ya fara iza shi, sa'ad da yake a zangon Dan, tsakanin Zora da Eshtawol.


'Yan'uwansa da dukan danginsa, suka gangara, suka ɗauki gawarsa, suka binne a kabarin Zora da Eshtawol. Samson ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin.


Akwai wani mutum a ƙasar tudu ta Ifraimu, da ake kira Mika.


Mutum ɗari shida daga kabilar Dan suka yi shirin yaƙi, suka kama hanya daga Zora da Eshtawol.


Daga can suka wuce zuwa ƙasar tudu ta Ifraimu, suka zo gidan Mika.


Sa'ad da suke a gidan Mika ɗin, sai suka ji muryar saurayin nan, Balawe, suka tsaya suka tambaye shi, “Wa ya kawo ka nan? Me kuma kake yi a nan?”


Da mutanen nan biyar suka koma wurin 'yan'uwansu a Zora da Eshtawol, sai 'yan'uwan suka tambaye su labarin tafiyarsu.


A lokacin nan ba sarki a Isra'ila. Sai wani Balawen da yake zama a wani lungu na ƙasar tudu ta Ifraimu ya ɗauko wata mace daga Baitalami ta Yahudiya ta zama ƙwarƙwararsa.


Balawen ya ce masa, “Muna tahowa ne daga Baitalami ta Yahudiya zuwa wani lungun da take ƙasar tudu ta Ifraimu, inda nake. Na je Baitalami ta Yahudiya ne, yanzu kuwa ina komawa gida. Ba wanda ya sauke ni a gidansa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan